Wani ma'aikacin Twitter ya rufe shafin Trump

Message on Twitter page that reads: "Sorry, that page doesn't exist!"

Asalin hoton, Twitter

Bayanan hoto,

For a short time visitors could only see a message that read: "Sorry, that page doesn't exist!"

Kamfanin Twitter ya ce an rufe shafin shugaban kasar Amurka Donald Trump na dan lokaci, amma tuni aka sake bude shi.

Wani ma'aikacin kamfanin ne ya rufe shafin na @realdonaldtrump, a ranarsa ta karshe ta barin aiki a kamfanin.

An rufe shafin na tsawon minti 11, amma a yanzu kamfanin na Twitter yana bincike kan hakan.

Shugaba Trump dai ya yi shakulatin bangaro da abin da ya farun a wani sabon sako da ya wallafa a shafin Twitter ranar Juma'a, abin da ke nuna irin tasirin da yake da shi.

A baya-bayan nan dai sakonnin da Mista Trump ke wallafawa a shafin Twitter na jawo ce-ce-ku-ce, inda yake da mabiya miliyan 41.7.

Wannan al'amarin na baya-bayan nan ya jawo muhawara sosai a kan tsaron da shafin shugaban kasar ke da shi, inda ake tunanin akwai yiwuwar nan gaba a dinga yada sakonnin karya da sunan Mista Trump.

Sai dai kuma hakan bai shafi shafin shugaban na gwamnati ba @POTUS.

'Ranar Karshe'

A ranar Alhamis da yamma ne wadanda suka leka shafin Mista Trump na dan lokaci suka ga wani sako da ke cewa: 'A yi mana afuwa, babu wanann shafin.!"

Asalin hoton, Twitter

Bayanan hoto,

Donald Trump has been actively using Twitter to promote his policies and attack his opponents

Bayan da aka dawo da shafin dai sakon farko na Mista Trump yana magana ne a kan shirin rage haraji na jam'iyyar Republican.

Kamfanin Twitter dai ya ce ba zai binciki wannan matsala ba, kuma zai dauki mataki don hana faruwarsa nan gaba.

Daga baya ya ce: "A bincikenmu mun gano cewa wani ma'aikacin kamfanin ne ya aikata hakan a ranarsa ta karshe ta barin aiki. A yanzu haka dai mun kaddamar da sahihin bincike."

'Wajen mayar da martani'

Mr Trump ya bude shafin Twitter ne a watan Maris na shekarar 2009 kuma ya wallafa sakonni fiye da sau 36,000.

Yana yawan amfani da shafin sada zumuntar don bayyana manufofinsa da kuma mayar da martani ga abokan hamayyarsa a lokacin yakin neman zaben 2016 da kuma bayan shan rantsuwar kama mulki a watan Janairun 2017.

A wata hira da aka yi da shi ya taba cewa, idan wani ya fadi wani abu a kansa, to zai je shafin Twitter ya kwankwashe shi ya mayar da martani a can.

Bayan da ya wallafa wani sako a Twitter a watan Satumba inda ya yi wa Koriya Ta Arewa barazanar rusata, an tursasa kamfanin Twitter ya bar sakon ba tare da goge shi ba.

Kamfanin ya ce sakon na Mista Trump ya cancanci yin labari a kansa.

Ko abokan Mista Trump ma ba su tsira ba wajen amfani da shafin Twitter.

Kamfanin ya taba dakatar da mai ba shi shawara a lokacin yakin neman zabe Roger Stone, bayan da ya yi amfani da kalamai marasa dadi ga manema labarai.