Shin ya dace a hallaka 'yan IS da iyalansu da aka kama?

Tutar IS

Asalin hoton, Getty Images

Kungiyar agaji ta Red Cross ta bukaci kasashen da ke fada da ta'addanci su yi la'akari da "hakkin dan Adam" a kan wadanda aka kama da sunan mayakan IS.

A lokacin da yake jawabi a Geneva, Daraktan kungiyar a Gabas ta Tsakiya, Patrick Hamilton, ya jaddada cewa dole a kiyaye dokokin duniya kan duk wani mataki da za a dauka a kan mayakan, tare yin watsi da kiran a hallaka su.

Ya amsa cewa yaki da IS ya bar baya da kura musamman kalubalen ayyukan jin kai.

Kuma duk da cewa Mista Hamilton ya yi la'akari da azabar da fararen hula suka fuskanta a karkashin gwamnatin IS a Mosul da Raqqa, musamman yake-yaken da aka yi a garuruwan, amma ya fi raja'a ne a kan makomar mayakan IS da aka kama da suka kunshi 'yan kasashen waje da suka tafi Syria da Iraki.

Red Cross ta ziyarci mata fiye da 1,300 da yara da dama da ake tsare da su kusa da garin Mosul, kuma ana tunanin iyalan mayaka ne a wasu kasashe da suka shiga IS.

Sannan yadda ake samun galaba a kan IS, akwai yiyuwar an kama iyalan mayakan kungiyar da dama.

Mece ce makomarsu?

Kungiyar agaji ta Red Cross ta ce Mista Hamilton ya damu da surutun jama'a game da dacewar a hallaka mayakan da iyalansu baki daya, inda ya ce bai dace a dauke su tamkar kamar ba mutane ba.

'Yan siyasa da dama a Birtaniya da Turai da suka kunshi manyan jami'an gwamnati sun ce hanya ma fi sauki da za a magance barazanar mayakan ita ce a hallaka su kawai.

Mutanen Turai dai na cike da fargaba da tsoro musamman wadanda suka tsira daga hare-haren da aka kai a Paris da Landan da New York a kan wadanda suka dawo yaki a Syria da Iraki.

An kiyasta kimanin mayaka 30,000 daga kasashen waje ne suka shiga IS, kuma masana tsaro na ganin daruruwansu da ke dawowa babbar barazana ce ga tsaron Turai.

Asalin hoton, Image copyrightUN/PAULO FILGUEIRAS

Bayanan hoto,

Agnes Callamard ta ce idan har ana son yin adalci ga mutanen da rikicin IS ya shafa, dole sai an bi tsarin shari'a

Sannan masanan na ganin tsare su a gidan yari ba zai haifar da "da mai ido ba" kamar yadda sakinsu zai tilastawa 'yan sanda sa ido sosai.

Amma Patrick Hamilton na Red Cross ya ce babu wani babban laifi da har zai sa a ki bin doka. A cewarsa ya kamata a kama mayakan, a tsare su idan sun aikata laifi a hukunta su.

Kungiyoyin kare hakkin bil'adama kamar Human Rights Watch na ganin irin yadda wasu kamar shugaban Amurka Donald Trump, ke matukar son ganin an kawo karshen IS baki daya, to za a iya rasa samun kwararan hujjojin ta'asar laifukan yaki da aka aikata.

Jami'ar Majalisar Dinkin Duniya Agnes Callamard, da ke bayar da rahoto a kan hukunce-hukuncen kisa da aka zartar ba kan ka'ida ba ta ce idan har ana son tabbatar da gaskiya da kuma yin adalci ga mutanen da rikicin IS ya shafa, dole sai an bi tsarin shari'a.

A nasa bangaren, Reed Broody na Human Rights Watch na ganin duk da cewa mayakan da aka kama barazana ne, amma kuma za a iya tatsar bayanai a kan IS musamman inda kungiyar ke samun tallafi da yadda ta ke tafiyar da lamurranta.

Yadda dai aka yi yaki kuma aka kawo karshensa yana da muhimmaci ga tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a nan gaba, in ji Mista Hamilton na Red Cross.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Birnin Raqqa ya kai shekara uku karkashin ikon IS