Adikon Zamani
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Yadda matar uba ta sa na bazama duniya

  • Akwai cikakkiyar tattaunawar da Fatima Zarah Umar ta yi kan wannan batu, sai ku latsa alamar lasifika da ke sama don sauraro.

Binta (wadda ba sunanta na asali ba ne) ta zauna a daki ita kadai.

Yanayin kunci da bakin cikin da take ciki, ya sanya dakin ya yi tsananin duhu fiye da ainihin duhun dakin.

Cikin shessheka da kokarin tsaida hawayen da yake fita daga idanunta ta hanyar amfani da takardar goge hannu ta share fuskarta tare da daidaita muryarta don fara ba ni lanarin rayuwarta...Hawayen ba su tsaya ba, muryarta na rawa ta fara magana:

"Na rasa mahaifiyata lokacin da nake da kananan shekaru kuma tun daga lokacin ban taba samun kwanciyar hankali ba a rayuwata."

Ta ci ga da cewa: "Mahaifina ya auri wata matar wadda ta rika gasa mana ukuba da ni da sauran 'yan uwana. A da yana da damuwa da mu, amma bayan da ya yi aure sai ya yi watsi da mu."

"Daga nan ne sai na fara yawace-yawace don neman hanyar da zan kula da kannena...a haka ne na hadu da wani mutum wanda ya yaudare ni."

"Ya yaudare ni, ya yi min ciki. Kuma ya matsa min lamba cewa sai na zubar da cikin amma sai na ki."

Binta ta ce mahaifinta ya goyi bayanta da farko, amma daga bisani sai ya "kore ta daga gidansu."

"A wannan gabar ce na fara shaye-shaye da kuma bin kawayen banza. Ba na kaunar irin wannan rayuwa. So nake na koma makaranta don na zama lauya."

Binta tana daya daga cikin dimbin yaran da wadansu iyaye ke watsi da su.

Wannan ne wani abu da ake yawan samu a arewacin Najeriya, inda iyaye da dama suke nuna halin ko in kula da ukubar da 'ya'yansu suke ciki.