Nigeria: Buhari ya ba da umarnin kulawa da Alex Ekwueme

Alex Ekwueme Hakkin mallakar hoto Getty Images

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ba da umarnin a duba lafiyar tsohon Mataimakin Shugaban Kasar Dokta Alex Ekwueme wanda yake jinya a kasar waje.

Matakin ya biyo bayan bayanin da shugaban ya samu ne ranar Juma'a game da halin jinyar da tsohon mataimakin shugaban yake ciki.

Umarnin da ya bayar ya kunshi ba shi jirgin da zai kai shi da kuma kudin maganin da za a yi masa a can.

Har ila yau shugaban ya yi fatan samun saukin Mista Ekwueme.

Mista Ekwueme shi ne ya yi wa tsohon Shugaban Najeriya Alhaji Shehu Shagari mataimakin shugaban kasa a tsakanin shekarun 1979 zuwa 1983, inda Muhamammadu Buhari ya kifar da gwamnatinsu.

Wannan matakin da Shugaba Buhari ya dauka ya zo daidai lokacin da wadansu 'yan kasar suke kokawa da tabarbarewa bangaren kiwon lafiyar kasar, abin da yake sa masu hannu da shuni fita kasashen ketare don neman magani.

Labarai masu alaka