Labarin fatalwa na Maimuna S Beli ya lashe Gasar Hikayata

Maimuna Idris Sani Beli ce ta lashe Gasar Rubutun Kagaggun Labarai ta Mata ta BBC Hausa
Bayanan hoto,

Maimuna Idris Sani Beli ce ta lashe Gasar Rubutun Kagaggun Labarai ta Mata ta BBC Hausa

Maimuna Idris Sani Beli ce ta lashe Gasar Rubutun Kagaggun Labarai ta Mata ta BBC Hausa, wato Hikayata, in ji alkalan gasar.

Alkalan uku dai sun zabo labarin marubuciyar ne daga cikin labarai 25 din da aka tantance aka mika musu a watan jiya.

Wadda ta zo ta biyu kuma ita ce Balkisu Sani Makaranta, da labarinta mai suna "Zawarcina".

San nan sai labarin "Sana'a Sa'a" wanda na hadin gwiwa ne tsakanin Habiba Abubakar da Hindatu Sama'ila Nabame Argungu.

"Fasalin bayar da labarin", a cewar jagoran alkalan, Farfesa Ibrahim Malumfashi, "da yadda ya ginu, da yadda aka fita daga duniyar da muke ciki aka koma lahira; daga lahirar aka dawo Najeriya, a cikin Najeriyar kuma aka bi wurare daban-daban aka gina labarin."

Ya ce shi ne babban dalilinsu na zabo "Bai Kai Zuci Ba" a matsayin labarin da ya yi zarra.

Bayanan bidiyo,

Bayanin alkalin gasar Hikayata kan labaran da suka yi nasara

Labarin da ya yi na daya:

Bai Kai Zuci Ba

Labarin da ya yi na biyu:

Zawarcina

Bayanan hoto,

Wadda ta zo ta biyu kuma ita ce Balkisu Sani Makaranta, da labarinta mai suna "Zawarcina

Labarin da ya yi na uku:

Sana'a Sa'a

Bayanan hoto,

Habiba Abubakar da Hindatu Sama'ila Nabame Argungu ne suka yi na uku a labarin hadin gwiwa da suka shigar

Labaran da suka cancanci yabo:

 • Garin Neman Gira
 • Hangen Dala
 • Labarin Ladidi
 • Mafarkin Uwa
 • Adikon Zamani
 • Almajiri
 • Matsalarmu
 • Dubu ta Cika
 • Sanadi
 • Direban Hajiya
 • Tsalle Daya
 • Karfin Hali

Farfesa Malumfashi, wanda masani ne kuma babban malamin jami'a a kan adabin Hausa, ya kuma ce alkalan sun tafka muhawara kafin sun yanke shawara a kan labarin da ya cancanci hawa matsayi na daya, saboda duk labaran sun yi kyau.

Alkalan, wadanda suka hada da Hajiya Balaraba Ramat Yakubu, (wadda fitacciyar marubuciya ce kuma mai shirya fina-finan Hausa).

Sai Hajiya Rahma Abdulmajid, (wadda fitacciyar marubuciya ce kuma mai sharhi a kan adabin Hausa), da Farfesa Ibrahim Malumfashi, sun kuma fitar da wadansu labaran guda 12 wadanda suka cancanci yabo.

A watanni masu zuwa za a karanta labaran da suka yi na daya da na biyu da na uku da ma wadanda suka cancanci yabon su 12 a shirye-shiryen Sashen Hausa na BBC.

Nan gaba a wannan watan ne dai za a bai wa wadannan marubuta da suka yi nasara kyautar kudi da lambobin yabo yayin wani biki a Abuja, babban birnin Najeriya.

Labarai kusan 400 aka tantance wadanda aka aiko daga sassa daban-daban na duniya.

Bayanan hoto,

Aisha Sabitu ce ta lashe kyautar bara

A bara ne dai Sashen Hausa na BBC ya kirkiro gasar ta Hikayata da nufin bai wa mata damar bayyana abin da ya fi damunsu a rayuwa.