Yadda masu kansar mama ke amfani da soso a kirjinsu

Wata kungiyar mata ta wadanda suka taba yin fama da cutar Sankara a kasar Kenya tana samar da soso don matan da aka yanke wa mama su yi amfani da shi a kirjinsu a madadin wanda aka yanke musu.

Wata da ta taba fama da cutar Sankarar, Anne Nyambura, ta ce ba ta jin dadin amfani da maman roba kuma wanda ake samarwa da soso ya fi ye mata dadin sanyawa a kirjinta.