'An wawure kudin yaki da Ebola' - Red Cross

Red Cross

Asalin hoton, Getty Images

Gamayyar kungiyoyin agaji ta Red Cross da Red Crescent ta ce tana da hujjar cewa an wawure dubban miliyoyin dala na kudaden tallafi da aka samar a shekarun 2014 zuwa 2016 lokacin annobar Ebola da ya addabi yankin Afirka ta Yamma.

Wannan annobar ta yi sanadiyyar mutuwar akalla mutane 10,000, kuma a lokacin kungiyar Red Cross ta samar da kimanin fam miliyan 76 daga babban ofishinta dake birnin Geneva ga kungiyoyin Red Cross dake kasashen Laberiya da Saliyo da kuma Guinea.

An ware kudin ne domin tallafawa asibitocin dake kula da masu cutar Ebola da dabarun birne wadanda suka mutu.

A lokacin annobar ta Ebola, ma'aikatan Red Cross sun rika sadaukar da kansu domin ceto rayukan wasu.

An samar da miliyoyin fam, amma labarin cewa an sace wasu daga cikin kudaden ya fito ne a shafin kungiyar na yanar gizo:

Ana cigaba da bincike, amma da alama cewa a Laberiya, fiye da fam milyan biyu sun yi dabo, kuma a Saliyo kusan fam miliyan 1.5 kana a Guinea akalla fam miliyan daya aka wawure.

Da aka tambayi babban sakataren kungiyar Red Cross, ElHadj as Sy ya ce kamata yayi a mai da hankali kan nasarorin da aka samu maimakon wannan batun:

"Sama da kashi 90 cikin 100 na kudaden da aka samar anyi amfani da su ne ta hanyoyin taimaka wa wadanda suka yi fama da cutar...amma batun yayi mana ciwo domin abin takaici ne, kuma bamu ji dadin lamarin ba".

Kungiyoyi masu bada taimako kamar Red Cross sun dogara ga kamfanoni masu bada taimako domin gudanar da ayyukanta a kasashen duniya.

Kuma a sanadiyyar wannan almundahanar, kungiyar ta samar da sabbin dabaru da take fatar zai ba masu bata tallafi karfin gwuiwar cigaba da taimaka mata.