Ana zargin ma'aikatan MDD da cin zarafin mutane

Ana zargin wasu sojojin wanzar da zaman lafiya na MDD da cin zarafin mutane a wasu kasashen duniya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ana zargin wasu sojojin wanzar da zaman lafiya na MDD da cin zarafin mutane a wasu kasashen duniya

Majalisar Dinkin Duniya ta ce ta karbi wasu sabbin bayanai kan zargin cin zarafi ta hanyar lalata da ake yiwa wasu ma'aikatanta da ke aiki a wasu kasashen duniya a cikin watani uku da suka gabata.

Akwai zargi guda 12 da ake yi wa sojojin wanzar da lafiyarta da ke Haiti da kuma wasu kasashen Afrika biyar, ciki har da Mali da jamhuriyar tsakiyar Afrika da kuma Sudan ta Kudu.

Sauran sun hada da Jamhuriyar dimukradiyar Congo da Liberia.

An kuma gabatarwa hukumar kula da masu gudun hijira ta MDD sabbin tuhumce tuhumce 15 da suka shafi wasu ma'aikatanta su uku da ke aiki a hukumar kula da masu kaura ta duniya da kuma asusun kula da yara kanana na Unicef.

Sai dai mai magana da yawun sakatare janarar na MDDR Stepeh Dujaric ya ce kawo yanzu ba a tabbatar da zargin da ake yi mu su ba.