An kai wa Saudiyya harin makami mai linzami daga Yemen

Riyadh

Asalin hoton, Getty Images

An jiyo karar fashewar wani abu a kusa da filin jirgin saman birnin Riyadh, yayin da wadansu rahotanni suke cewa dakarun kasar ne suka dakile wani hari daga kasar Yemen.

Kafar yada labarai ta Al-Arabiya ta ruwaito cewa sojin saman kasar ne suka dakile wani hari a arewa-maso-gabashin birnin Riyadh.

Wani gidan talabijin ya danganta harin da 'yan tawayen Houthi da ke kasar Yemen kuma ya ce an kai harin ne a filin jirgin saman birnin.

A baya dakarun Saudiyya sun sha dakile harin makami mai linzami wanda 'yan tawayen ke kai wa kasar.

Babu dai labarin barnar da harin ya jawo ko kuma asarar rai tukuna.

An kwashe shekaru ana fafata wa tsakanin dakarun gwamnatin Shugaban Yemen Abdrabbuh Mansour Hadi da kuma 'yan tawayen Houthi.

Saudiyya dai tana jagorantar yaki da 'yan tawayen ne.

Karanta wadansu karin labarai