Rayuwata na cikin hadari- Hariri

Saad Hariri ya ce yana fargaba game da tsaron lafiyarsa

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Saad Hariri ya ce yana fargaba game da tsaron lafiyarsa

Fira ministan Lebanon, Saad al Hariri ya ajiye mukaminsa, inda a wani gidan talibijin dake Saudiyya ya bayyana cewa yana fargaba game da tsaron lafiyarsa, ya yinda kuma ya caccaki kasar Iran.

Ya zargi Iran da saka tsoro a zukatan jama'a tare da yin barna a kasashe da dama, ciki harda Lebanon.

A shekarar 2005 ne aka kashe mahaifin Mr Hariri wanda shi ne tsohon fira ministan kasar watau Rafik al Hariri.

Iyalin Hariri nada kusanci sosai da Saudiyya , wadda suke gogaya da Iran a yankin gabas ta tsakiya.

Tun a shekarar 2016 ne Hariri ya zama fira minista koda yake a baya ya taba rike mukamin daga shekarar 2009 zuwa 2011.

"Muna rayuwa a cikin yanayi irin wanda ya kunno kai kafin aka hallaka Rafik al Hariri" ya ce a wani gidan talibijin dake Saudiyya.

Ya kuma soki kungiyar Hezbollah dake samun goyon bayan Iran wadda take tasiri a kasar ta Lebanon.

Sai dai Iran ta musanta zargin.

Ta ce magana ce da bata da tushe amma kuma ta ce murabus din da ya yi, abu ne da zai kara janyo zaman doya da manja a yanki.