'Abin da ya sa aka kama ministocin Saudiyya'

Saudi Arabian Prince Miteb bin Abdullah at the Elysee Palace in Paris, 18 June 2014

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

An sauya Yarima Miteb bin Abdullah daga mukaminsa na shugaban dakarun kasar

Tun bayan kama ministoci hudu da kuma yarimomin gidan sarautar Saudiyya 11 kan zargin cin hanci, ake sharhi kan hakikanin abin da ya jawo hakan.

Mohammad Qaddam Siddiq Isa wani mai sharhi ne a kan al'amuran da suka shafi yankin Gabas ta Tsakiya ya ce siyasar cikin gidan masarautar ce ta sa aka kama ministocin.

Sabanin yadda ake fada cewa "matsala ce ta cin hanci a'a, abin ya fi kama da siyasa," a cewarsa.

Latsa alamar lasifika da ke kasa don sauraron cikakkiyar hirarsa da BBC

Bayanan sauti

'Ana share wa yarima mai jiran gado hanya ne'

An kama su ne sa'o'i kadan bayan kaddamar da kwamitin wanda Yarima Mai Jiran Gado Muhammad bin Salman yake jagoranta.

Yarima Alwaleed bin Talal wanda biloniya ne da ke da hannun jari a kamfanonin Twitter da kuma Apple, yana cikin wadanda aka tsare.

Hakazalika Sarkin Salman ya sauya shugabannin dakarun tsaron kasar da kuma na sojin ruwa.

Sabuwar dokar yaki da cin hancin ta ayyana cewa: "Kasar nan ba za ta dore ba matukar ba mu magance cin hanci da kuma binciken wadanda suke aika ta shi ba."

Yarima Muhammad yana kokarin kara karfin ikonsa ne yayin da yake kara kawo sauye-sauye a masarautar kasar, kamar yadda wakilin BBC kan harkokin tsaro Frank Gardner ya ce.

Sabon kwamitin yana da ikon tsarewa da kuma haramta tafiye-tafiye ga wadanda ake zargi da cin hanci, a cewar kafar yada labaran kasar.

Sai dai ba a bayyana abin da ake zarginsu da aikatawa ba tukuna.

Amma kafar yada labarai ta Al-Arabiya ta ce an fara wani bincike kan ambaliyar ruwan da aka yi a birnin Jeddah a shekarar 2009 da kuma barkewar cutar Mers wadda aka yi a shekarar 2012.