Hotunan abin da ya faru a Nigeria a makon jiya

Hotunan wasu daga cikin manyan abubuwan da suka faru a sassa Najeriya daban-daban a makon jiya.

Shugaban Najeriya Muhammmadu Buhari da Mataimakinsa Yemi Osinbajo lokacin da suka halarci taron kwamitin koli na jam'iyyar APC a Abuja ranar Talata

Asalin hoton, Nigeria Presidency

Bayanan hoto,

Shugaban Najeriya Muhammmadu Buhari da Mataimakinsa Yemi Osinbajo lokacin da suka halarci taron kwamitin koli na jam'iyyar APC a Abuja ranar Talata

Asalin hoton, Lagos State Goverment

Bayanan hoto,

Jami'an hukumar LASEMA ta jihar Legas yayin da suke kwashe wadansu motocin bayan wani hadari a kan titin zuwa unguwar Ikorodu ranar Juma'a

Asalin hoton, Lagos State Goverment

Bayanan hoto,

Jami'an hukumar sun yi nasarar ceto mutane tara daga hadarin

Asalin hoton, Nigeria/Presidency

Bayanan hoto,

Tsohon Shugaban Ghana John Dramani Mahama lokacin da ya kawo wa Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ziyara a fadarsa da ke Abuja ranar Alhamis.

Asalin hoton, Borno State Government

Bayanan hoto,

Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima yayin da Sarauniyar Máxima Cerruti ta masarautar kasar Netherlands ta kawo masa ziyara a Maiduguri ranar Juma'a

Asalin hoton, Nigeria/Presidency

Bayanan hoto,

Sabon Sakataren Gwamnatin Najeriya Boss Gida Mustapha bayan ya karbi rantsuwar kama aiki a fadar shugaban kasa ranar Laraba

Asalin hoton, Sokoto State Goverment

Bayanan hoto,

Dalibai da suka kammala aikin yi wa kasa hidima a Najeriya yayin da suka kai wa Gwmnan jihar Sakkwato Aminu Tambuwal kyautar zanen shi da suka yi a fadarsa da ke Sakkwato ranar Asabar

Asalin hoton, DG Media

Bayanan hoto,

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje lokacin da tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya kai masa ziyara a gidan gwamnatin Kano da ke Abuja ranar Juma'a

Asalin hoton, Sokoto State Goverment

Bayanan hoto,

Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Tambuwal yayin da yake karrama Kwamishinan Ilimi Mai Zurfi na jihar, Alhaji Sahabi Isa Gada, wanda aka nada jakadan Najeriya a kasar Tanzaniya ranar Asabar

Asalin hoton, Sokoto State Goverment

Bayanan hoto,

Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Tambuwal yayin liyafar karrama sabon jakadan Najeriya a kasar Tanzaniya Alhaji Sahabi ranar Asabar