Nigeria: Yadda gurgu ke koya wa masu kafa sana'a a Abuja

Tukur Abubakar wani mutum ne wanda cutar Polio ta nakasa kafafunsa, sai dai ga alama zuciyarsa ba ta mutu ba.

Tukur wanda ya ce lalurar rashin kafa ta same shi ne tun yana karami, yana da yara da dama wadanda suke koyon aiki daga wurinsa.