Paradise Papers: An tona asirin manyan attajiran da ke kauce wa biyan haraji

  • Daga 'Yan Jaridan da ke aiki kan bayanan Paradise Papers
  • BBC Panorama
The Queen inspects the King's Troop Royal Horse Artillery outside Hyde Park Barracks in London, Britain, 19 October 2017

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Bayanan sirrin sun nuna cewa Sarauniyar Ingila ta zuba jarin fam miliyan 10 a kasashen ketare

Wadansu tarin bayanai sirrin harkokin hada-hadar kudi sun bayyana yadda manyan mutane ciki har da kamfanonin Sarauniyar Ingila na kashin kanta, inda suka zuba jari a wadansu wurare da ba a biyan haraji.

Hakazalika sakataren kasuwancin Shugaba Donald Trump yana da hannun jari a wani kamfanin da takunkumin da Amurka ta kakaba wa Rasha ya shafa.

Bayanan sirrin wadanda aka yi wa lakabi da Paradise Papers sun kunshi bayanai fiye da miliyan 13.

Shirin talabijin na BBC Panorama yana cikin kafafen yada labarai 100 da suke binciken wadannan takardun.

Kamar yadda shirin Panorama ya samu irin wadannan bayanan sirri a baya, a wannan karon ma jaridar kasar Jamus ta Süddeutsche Zeitung, ita ce ke jagoranci binciken.

Bayanan da aka samu ranar Lahadi yana daya daga cikin dimbin bayanan da suka tona asirin daruruwan mutanen da kamfanoni wadanda wasunsu suna da alaka da Birtaniya.

Yawancin labarin ya fi mayar da hankali ne ga 'yan siyasa da manyan kamfanoni da shahararrun mutane da cibiyoyi wadanda suke boye dukiyarsu daga biyan haraji, ko kuma boye cinikayyar da suka yi.

Galibin abin da suka yi bai saba wa doka ba.

Sauran manyan labaran da aka samu ranar Lahadi su ne:

  • An danganta wani na kusa da Firaministan Kanada da wani abu da ya jawo wa kasar miliyoyin daloli na haraji, inda hakan yake barazana ga firaministan wanda ya yi alkawarin magance kaucewa biyan haraji
  • Tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar Conservative Lord Ashcroft ya nuna halin ko in kula kan yadda ake tafiyar da harkokin da ya zuba jari a kasashen waje.
  • Sai batun kudin tafiyar da kungiyar kwallon kafa ta Everton

Sauran kafafen yada labarai za su yi labarai ne da suka shafi yankunan su.

Yadda Sarauniya ta shiga cikin lamarin?

Bayanan sirrin sun nuna cewa Sarauniyar Ingila ta juba jari a wani kamfanin kashin kanta kimanin fam miliyan 10 (dala miliyan 13).

An zuba kudin ne a tsibirin Cayman Islands da kuma Bermuda ta hannun kamfanin Duchy of Lancaster, wanda yake ba Sarauniyar kudin shiga kuma yake tafiyar da kamfanonin da kudinsu ya tasan ma fam miliyan 500.

Babu wani abu da ke nuna cewa Sarauniyar ta aikata ba daidai ba, ko kuma ba ta biyan haraji, amma abin tambayar shi ne ko Sarauniyar za ta iya zuba jari a kamfanonin kasashen ketare.

Asalin hoton, Alamy

Bayanan hoto,

Sarauniya tana da karamin hannun jari a kamfanin BrightHouse

Yankin Duchy ya ce bai san abin da ake yi da kudin ba, kuma akwai alamun da ke nuna cewa Sarauniyar ba ta da masaniya game da harkokin zuba jarin wadanda aka yi a madadinta.

Yankin ya sha cewa a baya "ya damu da duk wani abu da zai jawo zubewar kimar Sarauniyar, wadda ta damu da kamfanin."

Abin kunya ga Ross da Trump

Wilbur Ross ya taba taimaka wa Donald Trump yayin da ya kama hanyar ciyacewa a shekarun 1990, kuma Trump ya saka masa da mukamin sakataren kasuwanci a gwamnatinsa.

Bayan sun nuna cewa Mista Ross yana da jari a wani kamfanin jirgin ruwa na jigilar kaya wanda ya samu ribar miliyoyin daloli a shekara wajen sufirin mai da iskar gas na wani kamfanin makamashi na kasar Rasha, wanda surukin Shugaban Rasha ne Vladimir Putin da wadansu mutane biyu da takunkumin Amurka kan Rasha ya shafa.

Wannan zai kara ta da tambayar alakar da ke tsakanin Rasha da gwamnatin Donald Trump. Shugabancin Trump yana shan suka kan yadda ake zargin Rasha na da hunnu kan sakamakon zaben da aka yi a Amurka a shekarar 2015. Trump ya ce zarge-zargen "labaran karya ne".

Daga ina aka samu wadannan bayanan sirrin?

Galibin bayanan da aka samu an same su ne daga wani kamfani mai suna Appleby, wani kamfanin lauyoyi wanda ya taimakawa mutane kafa famfanoni wadanda ba sa biyan haraji koda ko na sisin kwabo.

Bayanansa da kuma sauran bisa hurumin dokokin kamfanonin yankin Caribbean, an same su ne daga kamfanin jaridar Süddeutsche Zeitung. Sai dai ba ta bayyana tushen labarinta ba.

Abokan bincikensu na kafofin yada labarai sun kwarmata bayanai daga wadannan kasashen ketare wadanda suke aikata ba daidai ba.

A wani martini ga bayanan sirrin, Appleby ya ce "ya gamsu babu wasu hujjoji da ke nuna an aikata ba daidai ba, daga bangarenmu ko kuma mutanen da muke hulda da su don mu ba ma maraba da dabi'un da suka saba wa doka."

Mene ne harkar hada-hadar kudi a tsibiran da ba a biyan haraji?

Hakan yaana nufin wani tsibiri da ke wajen kasarka ta asali inda dokokin kasar ba sa aiki don mutane ko kamfanonin da za su iya sauya hanyar kudi, ko dukiya don su amfana daga kaucewa biyan haraji.

Wannan shi ne wani wuri da ba a biyan haraji, ko kuma wadansu cibiyoyin kudi na kasashen ketare (OFCs). Wadansu wurare ne kanana da ke aiki a asirce kuma ya danganta kan yadda suke nazarin aikata ba daidai ba.

Birtaniya ita ce babbar wadda take sahun gaba a nan saboda yawancin tsibiranta da ke wajen kasar cibiyoyin kudi ne na kasashen ketare, amma lauyoyinsu da ma'aikatan bankuna da ke aiki a cibiyoyin suna zaune ne a birnin Landan.

A nan ana maganar manyan attajirai ne. Brooke Harrington wanda ya rubuta wani littafi mai suna, Capital Without Borders: Wealth Managers and the One Percent, ya ce kamfanonin kasashen ketare ba su kai kaso daya cikin 100 na dala 500,000 da ake bukata na kudin kamfanonin ba.

Mene ne tasirin hakan a kanmu kuma me ya sa muka damu?

A gaskiya kudi mai yawa. Kamfanin Boston Consulting Group ya ce ya kai kimanin dala tiriliyan 10 da ke ajiye a irin wadannan kamfanoni. Abin da ya kusa karfin tattalin arzikin kasar Birtaniya da Japan da kuma Faransa idan aka hada. Hakan zai iya zama wani adadi ne na masu ra'ayin rikau.

Masu sukar kamfanin da ke wadannan tsibiran sun ce wani abu ne da aka bari a asirce - wanda ya ba da kafar aikata ba daidai ba - da kuma nuna bambanci.

Sun kuma ce matakan gwamnati na magance abin ba sa aiki kuma ma suna tafiyar hawainiya.

Brooke Harrington ya ce idan attajirai suna kaucewa biyan haraji, masu karamin karfi ne ke biyan nasu:

"Akwai abin da gwamnati take bukata don ta yi aiki kuma tana samun hakan ne daga attajirai da kuma kamfanoni da ba sa boye harkokinsu."

Meg Hillier, dan majalisar Birtaniya kuma shugaban kwamitin kashe kudin al'umma ya shaida wa shirin Panorama cewa:

"Muna son mu fahimci abin da ke fita daga kasarmu, saboda idan da a ce ba a boye komai ba, to da wuya irin wannan abin zai faru… muna bukatar a tsage gaskiya da kuma baje komai a faifai."

Ko wadannan tsibirai sun kare kansu?

Wadannan cibiyoyin hada-hadar kudi na tsibirai sun ce idan da babu su azahiri, to babu wata maganar tarnaki wajen batun biyan haraji. Sun ce ba suna zaune a kan wasu makudan kudi da aka boye ba ne, amma su kawai dillalai ne na rarraba kudi a fadin duniya.

Bob Richards, wanda shi ministan kudi na tsibirin Bermuda yayin da shirin Panorama ya gana da shi ya ce ba aikinsa ba ne ya karbar wa wata kasa haraji, don haka sai su neman wa kansu mafita.

Da shi da kuma Howard Quayle, wato babban ministan tsibirin Isle of Man, wanda shi ma ya gana da shirin Panorama wanda shi ma ya taka muhimmiyar rawa wajen tono bayanan sirrin, ya ce ba su da hurumi kuma ya ce tsibiran da ba a karbar haraji ana sanya ido a kansu kuma suna bin dokokin hada-hadar kudi na duniya.

Kamfanin ya taba cewa tsibiran da ba sa karbar haraji suna "kare mutane masu laifi ne daga tsangwama ta hanyar su daga gwamnatocin masu cin hanci da rashawa".