Takardun Paradise: Dukiyar Sarauniya na jibge a tsibiran da babu haraji

The Queen Hakkin mallakar hoto Getty Images

Takardun kwarmato na Paradise sun nuna cewa an zuba jarin dukiyar Sarauniyar Ingila kimanin fam miliyan goma a wasu tsibirai na kasashen waje.

Harkokin rukunin gidajen basarakiyar na Duchy of Lancaster, wanda ke samar wa Sarauniya kudaden shigarta, ana ajiye su ne a tsibiran Cayman da Bermuda.

Wani bangare na wannan kudi ya shiga hannun wani kamfani da ke tafiyar da harkokin kasuwancin BrightHouse, wanda aka zarga da ci-da-gumin abokan huldarsa masu karamin karfi, har ya kai ga durkushewa da bashin fiye da fam miliyan 17 a kan shi.

Masu kula da rukunin gidajen sun ce kamfanin BrightHouse ba shi da hannu a shawarar zuba jari da wadannan kudi.

Babban jami'in harkokin kudi na rukunin gidajen fam miliyan 500 na Sarauniya, Chris Adcock, ya fada wa BBC: "Tsarin zuba jarinmu ya dogara ne a kan shawarwari daga manyan jami'an sa jarinmu...

"Kamfanin Sarauniya na zuba jari ne a harkoki na musammam da ake matukar ganin darajarsu sakamakon shawara daga manyan jami'an kula da harkokinmu na zuba jari."

Mai magana da yawun rukunin gidajen Sarauniya na Duchy of Lancaster ya kara da cewa: "Akwai bangarori da dama wadanda muka zuba jari kuma kalilan a cikinsu na can a ketare. Ana gudanar da cikakken binciken kudi kan duk harkokinmu na zuba jari kuma halastattu ne.

"Sarauniya bisa radin kanta take biyan haraji kan duk kudaden shigar da ta samu daga harkokin rukunin gidajenta."

Kimar kamfanin gidajen Sarauniya

Bayanai game da hada-hadar zuba jarin kamfanin rukunin gidajen Sarauniya ya fito fili ne a cikin takardun tonon silili na Paradise - wasu takardun kwarmato ne guda miliyan 13 da dubu 400 daga wasu kamfanoni ciki har da Appleby, daya daga cikin manyan kamfanonin lauyoyi masu hada-hadar zuba jari na ketare a duniya.

Ana ajiyar asusun guda biyu ne a iyakokin Burtaniya na ketare ba tare da biyan harajin kamfani ba.

Sai dai kamfanin rukunin gidajen Sarauniya ya ce ba shi da masaniya cewa akwai moriyar da ake samu ta haraji a irin wadannan asusu da aka zuba na ketare, ya kara da cewa dabarar ririta biyan haraji ba ta cikin manufar zuba jari ta rukunin gidaje.

Takardun sun nuna yadda kamfanin rukunin gidajen Duchy of Lancaster ya sa fam miliyan biyar a wani asusu da ke Bermuda cikin shekara ta 2004, ya kuma kammala harka a shekara ta 2010.

A shekara ta 2005 kamfanin ya amince ya sanya dala miliyan 7 da rabi a wani asusu da ke tsibirin Cayman.

Takardun sun nuna an zuba dukiyar ce a kamfanonin fasaha da harkar likitanci.

Alakarsa da kamfanin mallaki gidan da kake ciki na BrightHouse ta fara ne a 2007 lokacin da kamfanin na Amurka da ke juya kudin ya nemi kamfanin gidajen Sarauniya ya zuba dala dubu 450 don aiwatar da wasu ayyuka guda biyar.

Wannan ya hadar da muradin sanya jari a wani kamfani mai sansani a London Vision Capital wanda ya saye hannun jarin BrightHouse da kuma kashi 75 cikin 100 na wani katafaren kantin sayayya na Threshers.

A karkashin wannan sabuwar yarjejeniya, litattafan hada-hada na kantin Threshers sun cika da basussuka kuma tsawon shekara biyu bai biya haraji ba.

Daga bisani jarin kamfanin Vision Capital na BrightHouse sai ya shiga hannun wani kamfani da ke Luxembourg kuma ya rika biyan harajin kamfani kalilan a Burtaniya.

A watan jiya kuma, sai Hukumar kula da Harkokin Kudi ta Burtaniya ta ce BrightHouse wanda ke sayar da kayan lantarki da kujeru na gida mafi rinjaye ga mutane masu karamin karfi ta hanyar biya kadan-kadan duk mako, bai nuna "dattako ba" don haka ta bukaci ya biya diyyar kimanin fam miliyan 15 ga abokan huldarsa mutum 249,000.

Rukunin gidajen Sarauniya na Duchy ya ce jarinsa a asusun tsibiran Cayman zai ci gaba da zama har shekara ta 2019 ko 2020, a lokaci guda kuma harkokinsa a kamfanin BrightHouse yanzu ya kai kashi 0.0006 cikin 100 na dukiyarsa. Kamfanin Sarauniyar bai bayar da jimillar kudi na harkokinsa a kamfanin Threshers ba.

Labarai masu alaka