Dan bindiga ya harbe mutum 26 a Amurka

Church Shooting
Image caption 'Yar babban limamin cocin, Annabelle na daga cikin mutanen da aka kashe a harin

An kashe akalla mutum 26 a wani hari da wani dan bindiga ya kai, inda ya bude wuta kan masu ibada a wata mujami'a da ke cikin jihar Texas in ji jami'ai a Amurka.

Ya fara harbi kan mai uwa da wabi ne daga wajen cocin, kafin ya shiga ciki ya bude wuta.

Gwamnan Texas, Gregg Abbott ya bayyana harin bindigar a matsayin mafi muni a tarihin jihar.

Yayin wani taron manema labarai a garin Sutherland Springs, Mista Gregg Abbott ya ce an raunata karin wasu mutanen kimanin 20 a wannan hari.

Wani mai magana da yawun sashen tsare rayuwar jama'a a Texas, Freeman Martin ya ce mutumin da ake zargi wanda a cewarsa farar fata ne kuma dan kasa da shekara 30 ya sanya rigar sulke da bakaken kayan fada.

Ya ce maharin ya yar da bindigarsa ya arce a cikin mota, bayan wani mazaunin yanki ya yi kukan kura ya rike bindigar inda harbe shi.

Daga bisani an gano shi mace a cikin motarsa wadda ke dauke da makamai birjik.

Kafofin yada labaran Amurka sun bayyana mahari a matsayin Devin P Kelley dan shekara 26, ko da yake zuwa yanzu 'yan sanda ba su tabbatar da hakan ba.

'Yan sanda sun ce wadanda aka kashen sun hadar da yara 'yan shekara biyar da kuma tsoffi 'yan kimanin shekara 72.

Shugaba Trump wanda ke ziyara a birnin Tokyo cikin kasar Japan ya bayyana ta'aziyyarsa kan abin da ya kira bakar wahalar da hankali ba zai iya kwatantawa ba ga mutanen da wannan iftila'i ya shafa.

Labarai masu alaka