Hatsarin jirgi ya yi ajalin yariman Saudiyya

Helicofter crash

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ba a bayyana adadin jami'an da suka mutu a hatsarin jirgin zuwa yanzu ba

Wani dan sarauta da manyan jami'an gwamnatin kasar Saudiyya da dama sun mutu a wani hatsarin jirgin shalkwafta a kusa da kan iyaka da Yemen, a cewar gidan talbijin din kasar.

Yarima Mansour bin Muqrin shi ne mataimakin gwamnan lardin Asir kuma dan tsohon yarima mai jiran gadon masarautar, Muqrin al-Saud.

Zuwa yanzu babu masaniya kan abin da ya janyo hatsarin jirgin a kusa da garin Abha da ke kudancin kasar.

Saudiyya ta ce ta tarbe wani makami mai linzami da aka harba cikin kasar daga Yemen, kusa da filin jiragen sama na Riyadh kwana guda kafin hatsarin jirgin.

A kuma karshen wannan mako ne, masarautar ta ce ta rufe asusun ajiyar banki na wasu 'ya'yan sarauta da ministoci da 'yan kasuwar da aka tsare ranar Asabar a wani al'amari na yin kakkaba a shugabancin Saudiyya.

Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman ne dai yake jagorantar hukumar yaki da cin hancin.

Mahaifinsa Sarki Salman ne ya tube uban yarima Mansour bin Muqrin, wanda ya rasu a hatsarin, watanni kalilan bayan ya hau kan mulki a 2015.

Rukunin jami'an na gudanar da wani rangadi ne ta sama a yankin lokacin da wannan iftila'i ya faru.