Kamfanoni 800,000 ba sa biyan haraji a Nigeria - Kemi Adeosun

Kemi Adeosun

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ministar ta kara da cewa a shekarar 2016 mutane 241 ne kawai suka biya haraji da ya kai Naira miliyan 20.

A yayin da Najeriya ke bin matakan rage dogaro da arzikin fetir, gwamnatin kasar ta ce ta gano kamfanoni kimanin 800,000 da ba su taba biyan haraji ba, wadanda da suka hada da na 'yan Kwangila.

Wata takarda da ministar kudin Najeriya Kemi Adeosun ta rubuta, kuma aka raba wa manema labarai kan hanyoyin bunkasa tattalin arzikin Najeriya, ta ce yanzu haka gwamnati na binciken kwakwaf a kan kamfanonin.

Sai dai kuma ba a bayyana sunayen kamfanonin ba, ko kuma irin ayyukan da suke yi.

Wani jami'in hukumar karbar haraji ta kasa ya shaidawa BBC cewa babban kalubalen da suke fuskanta shi ne gano adireshin kamfanonin duk da cewa suna da rijista.

Ya ce a reshen ofishin hukumar da yake kula da shi kawai a Ikoyi a Lagos, akwai kamfanoni sama da 8000 da aka gano cewa ba su taba biyan haraji ba.

Ko da yake Jami'in ya ce Lauyoyi ne ke taimaka wa kamfanonin kaucewa biyan haraji domin suna masu rijista ba tare da sun tantance adireshin da kamfanonin suke ba, da kuma manufar kafa kamfanin, lamarin da ke bai wa jami'an hukumar karbar harajin wahala.

Ministar kudin ta Najeriya ta ce gwamnati ta fi samun kudaden haraji daga albashin ma'aikata, wato kusan kashi 95 daga cikin miliyan 14 da ya kamata su biya haraji.

Ministar ta kara da cewa a shekarar 2016 mutane 241 ne kawai suka biya haraji da ya kai Naira miliyan 20.

"Arzikin fetir da Najeriya ke tinkaho da shi ne dai ya sa gwamnatocin da suka gabata suka yi sake wajen karfafa guiwar wasu hanyoyin samun kudaden shiga," a cewar Ministar.

Yanzu, ta ce Ma'aikatar kudi ta kaddamar da wani shiri na tattaro bayanai daga ofisoshin gwamnati, da na Bankuna, da hukumar kwastam, da kuma wadanda suka mallaki kamfanoni.