Shugaba Robert Mugabe ya kori mataimakinsa

shugaban Zimbabwe

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Shugaba Mugabe mai shekara 93, ya kwashe shekara 30 yana mulkin Zimbabwe

Ministan yada labarai na Zimbabwe SK Moyo, ya sanar da cewa Shugaba Robert Mugabe, ya kori mataimakinsa Emmerson Mnangagwa nan take.

Mista Moyo ya ce hujjoji sun nuna karara cewa Mr Mnangagwa ba ya tafiyar da ayyukansa yadda ya kamata.

Ya ce: "Korarren mataimakin shugaban kasar ya nuna rashin biyayya ga shugaban kasar."

Dama dai mataimakin Mista Mugaben yana kara samun magoya baya a tsakanin 'ya'yan jam'iyyar Zanu PF mai mulkin kasar.

Magoya bayansa da dama sun yi wa matar shugaban kasar ihu a wani taron gangamin siyasa a ranar Asabar a garin Bulawayo, birni na biyu mafi girma a kasar.

Mugabe ya furta cewa, "Mnangagwa na da 'yancin jan magoya baya da kuma kafa tasa jam'iyyar".

To sai dai kuma, wannan lamari bai yi wa shugaban dadi ba.

A wurin wani taro, Shugaba Mugabe ya nuna rashin jin dadinsa a fili, inda ya yi bayani fuska yamutse, tare da cewa, "ba zai yarda ba da cin fuskar da magoya bayan mataimakin shugaban kasar ke yi masa ba".

Dama tun a lokacin ya bukaci mataimakin shugaban kasar da magoya bayansa da su yi masa da'a ko kuma ya kore shi daga kan mukaminsa.

A taron gangamin na ranar Asabar magoya bayan Mnangagwe sun yi wa matar shugaban ihu.

Abin da ya nemi ya kawo babbar baraka da tashin hankali tsakanin mutumin da ya yi imanin cewa shi zai gaji Mista Mugabe da kuma matar shugaban da ake ganin za ta iya zama mataimakiyar shugaban kasa.

Bangaren mata na jam'iyyar, wanda Grace Mugabe ke jagoranta, na kokarin sauya kudin tsarin mulkin jam'iyyar domin bai wa mata daya daga cikin gurabe biyu na mataimakin shugaban kasa.

Ana dai ganin hakan ka iya bai wa Misis Mugabe damar zamowa mataimakiyar mijinta.