An kashe dan Birtaniya da aka sace a Nigeria

Pollution in Niger Delta

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

A yankin Niger Delta aka sace Turawan na Birtaniya

An kashe wani dan Birtaniya da aka sace a jihar Delta da ke kudancin Najeriya, yayin da kuma aka kubutar da wasu guda uku, kamar yadda hukumomin Birtaniya suka tabbatar.

Ian Squire na cikin 'yan Birtaniya hudu da ake tunanin masu tayar da kayar baya a yankin Niger Delta ne suka yi garkuwa da su a ranar 13 ga watan Oktoba.

Ofishin jakadancin Birtaniya ya ce an kubutar da Aanna Carson da David Donovan da Shirley Donovan tare da taimakon hukumomin Najeriya.

Birtaniya ta ce hukumomin Najeriya suna gudanar da bincike domin gano wadanda suka yi garkuwa da mutanen, kuma ofishin jakadancin kasar zai yi iya kokarinsa domin taimakawa iyalan Turawan mishan din.

Babu dai wani bayani a kan ko an biya kudin fansa domin sakin Turawan Birtaniyan.

Bayan sakin mutanen, hukumomin Birtaniya sun yi gargadi ga 'yan kasar su kaucewa zuwa yankin Jihar Delta, saboda yawan sace-sacen mutane da ake yi a jihar.

Asalin hoton, BBC news online