EFCC ba ta bincike na – Sheikh Pantami

Pantami

Asalin hoton, Facebook/NITDA

Bayanan hoto,

Sheikh Pantami ya zama shugaban hukumar NITDA ne a shekarar 2016

Shugaban Hukumar bunkasa fasahar sadarwar ta zamani ta Najeriya (NITDA), Sheikh Isa Pantami, ya ce ba gaskiya ba ne batun da ake cewa Hukumar EFCC da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasar zagon kasa tana bincikensa.

Wadansu rahotanni da ba a tabbatar ba sun ruwaito Ministan Sadarwar kasar Adebayo Shittu yana cewa gwamnatin tarayya tana jiran sakamakon wani binciken da hukumar EFCC take wa shugabannin hukumar NITDA.

Rahotannin sun ce ana binciken hukumar ne kan yadda ta kashe kudin da aka ware mata a kasafin kudin shekarar 2017, bayan wani korafi da aka gabatar a gaban hukumar EFCC.

Sai dai Sheikh vPantami ya musanta hakan, "karya aka rubuta a kanmu kuma idan mun samu wadanda suka aikata hakan, to kotu za mu kaisu," in ji shi.

Ya ce hukumar EFCC ba ta taba bincikarsa ba ko wani ma'aikacinsa tun da ya kama aiki da hukumar NITDA.

"EFCC sanya mana albarka take game da kokarin da muke na kawo gyara a hukumar NITDA," kamar yadda ya ce.

Latsa alamar lasifika da ke kasa don sauraron cikakkiyar hirar da BBC ta yi da Sheikh Pantami kan batun:

Bayanan sauti

Albarka hukumar EFCC take sanya mana – Pantami

BBC ta tuntubi mai magana da yawun hukumar EFCC, Wilson Uwujaren, wanda ya ce: "ba zan iya cewa da gaske ne ana binciken hukumar NITDA ba, kuma ba zan iya cewa karya ba ne."

Karanta wadansu karin labarai