Shafin fallasa cin hanci ya fara aiki a Nigeria

Leak.ng Hakkin mallakar hoto Leaks.ng
Image caption Hadin gwiwar kungiyoyi ne a Najeriya suka kafa shafin wanda ya kunshi matakai don kwarmata cin hanci

Gamayyar kungiyoyin fafutuka, da kare hakkin bil'adam da 'yan jaridu a Najeriya sun bude wani shafin Internet don ba wa 'yan kasar damar fallasa mutanen da ake zargi da badakalar cin hanci da rashawa.

Shafin Leaks.ng zai zama wata kafa da 'yan Najeriya za su bayar da bayanan sirri, yayin da su kuma 'yan jarida za su dauki labarin su kwaza shi, su kuma kungiyoyin kare hakkin dan'adam su shiga fafutukar matsa lamba ga gwamnati ta bincika.

Wani jami'i cikin gamayyar Abdul'azeez Abdul'azeez ya ce: "Shafin zai taimaka wajen bankado mutanen da ke cin hanci da rashawa ko kuma suka aikata ba daidai ba, ta hanyar amfani da mukami don cimma bukatunsu na kashin kai ko kuma su saci dukiyar jama'a ko yin wani abu na almundahana da sauransu."

Ya ce an hadin gwiwar kungiyoyin kare hakkin dan'adam na Najeriya da ke aiki kan abin da ya shafi shugabanci nagari da yaki da cin hanci da rashawa da taimakon kafofin yada labarai a kasar.

Jami'in ya ce tsarinsu na da banbamci da manufar kwarmata bayanai ta gwamnatin Najeriya, inda ya ce bayanan da aka wallafa a shafin, zai kasance mafarin bincike ga 'yan jarida don yayata labarin.

A cewarsa: "Kamar shigen abin da aka yi kan binciken da ake kira 'Panama Papers, wanda ya kai ga bankado almundahanar kudi da aka tafka a duniya gaba daya."

Abdul'azeez Abdul'azeez ya ce shafin zai yi amfani da wasu takardu ko muhimman bayanai da masu zargi za su hada don tallafa wa ikirarin da suka yi a kan wani mutum ko jami'in gwamnati.

Ya ce sun yi amfani da tanade-tanaden boye masu amfani da shafin don kwarmata bayanan sirri ciki har da rashin bukatar bayar da bayanan sunan mai fallasar.

Cin hanci da rashawa manyan matsaloli ne a Najeriya kuma har ta kai shugaban kasar Muhammadu Buhari na ikirarin cewa "idan ba a kashe ta ba, to ita za ta kashe kasar.

Labarai masu alaka