PDP ta zargi gwamnatin Katsina da gaza tabuka abin kirki

APC ce ke mulkin Nigeria

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Jam'iya mai mulki a Nigeria

Jam`iyyar PDP mai adawa a Najeriya da kuma a Katsina ta yi zargin cewa tun lokacin da takwararta APC ta kwace mulkin jihar daga hannunta babu wani abin kirkin da ta tsinana wa jihar tsawon kimanin shekara uku.

Shugaban PDP a jihar Katsina, Alhaji Salisu Yusuf Majigiri ya ce ayyukan raya kasa sun tsaya cik, hatta wasu manyan ayyuka da gwamnatinsu ta fara aiwatarwa, amma ba ta kammala gabanin ta bar mulki ba, duk an yi watsi da su.

Ya ce ayyukan sun hadar da Kasuwar Dubai da kwalejin fasahar sadarwa, ya yi ikirarin cewa gwamnatin jihar ta fi mayar da hankali wajen runton aiki ta hanyar yi wa makarantun da gwamnatinsu ta gina fenti.

Haka zalika, PDP ta zargi jam'iyyar APC da karbo bashin biliyoyin naira ba tare da aiwatar da aikin a-zo-a-gani ba.

Sai dai APC ta musanta wadannan batutuwa, ta ce PDP ba ta da bakin magana idan aka yi la`akari da dumbin bashi da mawuyacin halin da ta bar al`ummar jihar a ciki.

Shi dai Majigiri na cewa: "Maganar ilmi da noma da kula da lafiya dukkansu ba bangaren da ya ci gaba, sai baya da muka mika mulki. Kuma mun bar kudi sun kai biliyan 14 a asusun gwamnati, sannan zuwa yanzu ta karbi sama da biliyan 300 amma a nuna min aikin wani aiki na miliyan 500 da za a iya budewa a jihar Katsina."

Ya ce makarantun da gwamnatinsu ta bari ne, jam'iyyar APC take bi tana yi musu fenti maimakon fentin Najeriya da suke da shi. A cewarsa: Da ya ji ruwan damuna zai wanke, fenti aiki ne?"

Shugaban jam`iyyar APC na jihar Katsina, Alhaji Shitu Shuaibu Shitu ya ce hasali ma, kura-kura da PDP ta tafka ne suka jefa Katsina a halin da ta samu kanta, don haka bai kamata ta zake tana hakikicewa ba.

Ya ce zamanin mulkin PDP, gwamnatinsu ba ta dauki hakkin ma`aikata a bakin komai ba, duk kuwa da irin gudummuwar da suke bayarwa wajen raya kasa da ciyar da jihar gaba.

Bayanan hoto,

PDP babbar jam'iyar adawa a Nigeria

Jam`iyyar PDP ta shafe shekara 16 tana mulkin jihar Katsina. Sai a 2015 ne ta sha kaye a hannun jam`iyyar APC.

Manufar caccaka da sukar da abokan adawar siyasa kan yi dai, kamar yadda masana ke cewa, ita ce ankarar da jam`iyya mai mulki don ta gyara tafiyarta.

Amma a Najeriya ba kasafai jami`yya mai mulki ke kallon lamarin a matsayin gyara kayanka ba, sakamakon zargin cewa ba da kyakkyawar niyya aboakan hamayya kan yi hakan ba.