Nigeria: Bukola Saraki ya musanta zargin kin biyan haraji

Saraki
Image caption A baya kotun da'ar ma'aikatan Najeriya ta wanke Saraki daga zargin yin karya wurin bayyana kadarorinsa

Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Bukola Saraki ya wanke kansa kan zargin kin biyan haraji da ake masa.

Wata sanarwa da mai magana da yawun Saraki Yusuph Olaniyonu ya aikewa manema labarai, ya kuma bayyana matsayin wani kamfaninsa da aka kwarmato cewa ya bude shi ne domin kaucewa biyan haraji.

Sanarwar ta danganta lamarin da siyasa domin ba ta sunan Sanata Saraki.

An wallafa Bukola Saraki cikin takardun Paradise da aka bankado, wanda shi ne mutum na uku mafi girman mukami a tsarin siyasar Najeriya, a matsayin wanda ya kafa kamfanin Tenia Limited a tsibirin Cayman Islands a shekarar 2001.

Kuma ya ci gaba da zama daraktan kamfanin da kuma mamallakinsa har zuwa shekarar 2015.

Tsibirin Cayman Islands dai ya shahara wajen boye kadadarorin wadanda ba sa san biyan haraji.

Ya ce mai gidansa bai saba doka ba kuma bude kamfanin bai saba wa ka'ida ba.

Ya kara da cewa An kafa Kamfanin ne a shekarar 2001 tun lokacin da Saraki bai ma shiga siyasa ba.

"Kamfanin bai taba aiki ba tun da aka kafa shi, bai taba mallakar wata kadara ba, bai yi ciniki ko kuma wani kasuwanci ba, kuma ba shi da wani asusu a Banki a iya sanin Saraki."

Mista Olaniyu ya ce idan har ma Kamfanin na da asusun Banki, to Saraki ba shi ke da iko da asusun ba.

Daga karshe sanarwar ta bukaci a yi watsi da zargin da ake kan an kafa kamfanin ne domin aikata wata zamba, ko hanyoyin da aka bi wajen kafa shi sun saba doka.

An tsegunta bayanan sirrin ne ga jaridar Sueddeutsche Zeitung ta Jamus, wacce ta bai wa kungiyar 'yan jarida masu bincike ta kasa da kasa (ICIJ) ciki har da BBC da jaridar Premium Times ta Najeriya.

Kuma kamar sauran 'yan siyasar duniya da sunansu ya fito a katardun Paradise Papers, wadannan bayanai ba za su yi wa Sanata Saraki dadin ji ba, ganin yadda yake sahun gaba wurin kiraye-kirayen a kawo sauyi domin inganta tsarin karbar haraji a kasar.

Labarai masu alaka