Mota ta afka aji, yara biyu sun mutu

'Yan sanda na binciken wani hadarin mota da ya faru a yankin Greenacre a garin Sydney. Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption 'Yan sanda na binciken wani hadarin mota da ya faru a yankin Greenacre a garin Sydney.

Wasu yara biyu maza 'yan shekara takwas sun mutu bayan da mota ta afka cikin wani aji a wata makarantar firamare a Sydney.

'Yan sandan kasar sun ce hadarin wanda da ya faru ne a makarantar gwamnati ta layin Bankisa ya raunata yara mata uku wadanda yanzu su na asibiti.

Hukumomi sun ce likitoci masu bada agajin gaggawa sun duba sauran yara 19 da ke ajin a take a wajen.

Matar da ke tuka motar wata mata ce 'yar shekara 52, kuma an kai ta caji ofis. Hukumomi a garin sun ce ba sa tunanin cewa hadarin ya faru ne da gangan.

Hadarin ya faru ne misalin 09:45 a ranar Talata (22:45) agogon GMT ranar Litinin a yankin Greenacre.

Likitoci masu bada agajin gaggawa sun bayyana inda hadarin ya faru a matsayin "waje mai tsananin rikicewa".

Wasu yara biyu maza 'yan shekara takwas sun mutu bayan da mota ta afka cikin wani aji a wata makarantar firamare a Sydney, in ji 'yan sanda.

Hadarin da ya faru a makarantar gwamnati ta layin Bankisa ya raunata yara mata uku wanda yanzu su na asibiti.

Hukumomi sun ce likitoci masu bada agajin gaggawa sun duba sauran yara 19 da ke ajin a take a wajen.

Wata mace 'yar shekara 52 ce take tuka motar, kuma an kai ta ofishin 'yan sanda. Hukumomi a garin sun ce ba sa tunanin hadarin ganganci ne.

Likitoci masu bada agajin gaggawa sun bayyana inda hadarin ya faru a matsayin "waje mai tsananin hadari".

"Bisa dukkan alama, waje ne na tsananin tashin hankali" a cewar wata ma'aikaciyar hukumar bayar da agaji na gaggawa na New South Wales (NSW) Ambulance Sufirtanda Stephanie Radnidge.

"An samu wasu yara da malamai da su ka shiga matsanancin tashin hankali da damuwa a wurin da hadarin ya faru".

Samun kula

An kai yaran maza biyu asibiti, inda a nan ne su ka rasu sakamakon raunukan da su ka samu. Wata yarinya 'yar shekara tara na cikin matsanancin hali, yayin da wadancan biyun 'yan shekara takwas sun samu sauki.

'Yan sanda sun ce kadan daga cikin yaran sun samu kananan raunuka kuma an kula da su a take a wajen da hadarin ya faru.

Abun na da tsananin wahala saboda mu kanmu iyaye ne, kuma mu mutane ne" in ji Sufirtanda Radnidge.

"Amma mu na da matukar horaswa kuma mun bayar da kulawa ta musamman ga wadnda su ka samu raunuka da safen nan."

'Yan sanda sun ce za a yi wa matukiyar motar gwaje-gwajen jini da na fitsari, kuma su na binciken yadda hadarin ya faru.

"Ba mu yarda cewar wannan hadarin da gangan ya faru ba" inji Shugaban 'Yan sanda na New South Wales, Kwamanda Stuart Smith.

Har yanzu dai hukumomi ba su kai ga tantance ko matar na da wata alaka da makarantar ba.

Wani mutum da ya ke wajen a lokacin da abun ya faru, Khaled Arnaout, ya ce, ya ga wani babban rami a jikin bangon ajin bayan da yai ta jin ihu na fitowa daga wajen.

Labarai masu alaka