Donald Trump ya sassauta ra'ayinsa kan Koriya Ta Arewa

Mr Trump da Mr Moon

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Mr Trump da Mr Moon sun tattauna a ranar Talata kan harkokin kasuwanci

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi kira ga Koriya Ta Arewa da ta yarda a hau teburin tattaunawa don hakura da batun shirin makami mai linzaminta.

Mista Trump ya furta hakan ne a wani taron manema labarai inda shi da shugaban Koriya Ta Kudu ke halarta, yayin wata ziyara da yake yi a Koriya Ta Kudun, mai cike da damuwa kan barazanar nukiliyar Koriya ta Arewa.

Sai dai a wannan karon ya sauya irin kalamai masu zafi da ya saba furtawa kan Koriya Ta Arewan, inda ya ce yana fatan a sulhunta ba tare da amfani da karfin soja ga Pyongyang ba.

Trump ya isa Seoul ne daga Tokyo bayan ya ce Japan na iya kakkabo makaman Koriya ta arewa masu linzami.

Mai aikowa BBC da rahotanni daga Seoul ya ce an tsara ziyarar Trump da nufin karfafa huldar soji, wacce da dadewa ta kasance kariya ga tsaron Koriya ta Kudu, musamman yanzu da kasar ke cike da barazanar makwabciyarta Koriya ta Arewa.

Mista Trump a ziyararsa ta baya a yankin Asiya ta gabas ya ce shi da shugaban Koriya ta Kudu Moon Jae-in, za su yi aiki kan wata dabara da za su bullo wa hukumomin birnin Pyongyang.

Sai dai kuma Shugabannin kasashen guda biyu sun samu dan sabani inda a baya, Trump ya soki Mista Moon da tsoron "a mutu" saboda yadda ya ke bin matakai na lallashin Koriya ta Arewa.

Tun da faro dai wakilin BBC ya ce 'yan Koriya ta Kudu da dama na fatan Trump zai kaucewa furta zafafan kalaman da ya saba yi kan Koriya ta Arewa.

Ya kuma ce an kaddamar da zanga-zanga masu karo da juna a Seoul kan ziyarar ta Mista Trump.

A daya bangaren, ziyarar Trump za ta kunshi sabunta huldar cinikayya tsakanin Amurka da aminiyarta Koriya ta Kudu.

Sannan shugaban na Amurka zai ziyarci China da Vietnam da Philippines a mako mai zuwa.