Sojoji sun yi arangama da 'yan Boko Haram a Adamawa

Sojojin Najeriya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Wadannan hare-haren dai sun nuna har yanzu kungiyar BH barazana ce a yankin arewa maso gabashin Najeriya

Wasu 'yan kunar bakin wake sun kai hari a Maiduguri, babban birnin jihar Borno da ke arewa maso gashin Najeriya a ranar Talata da safe.

Kawo yanzu 'yan kunar bakin waken da suka kai harin ne aka tabbatar da mutuwarsu, wadanda dukkaninsu mata ne.

Harin ya kuma yi sanadin da wasu mutum shida suka jikkata.

A wannan shekarar kadai birnin Maiduguri ya fuskanci hare-haren kunar bakin wake 58.

Harin na zuwa a yayin da hukumomi a jihar Adamawa da ke makwabtaka da jihar ta Borno suka ce jami'an tsaro sun fatattaki wasu mahara da ake zargin 'yan Boko Haram ne, bayan wani kazamin fada a daren ranar Litinin a garin Gulak.

'Yan Boko Haram sun kaddamar da harin ne a garin Gulak da tsakiyar dare, lamarin da ya tursasawa daruruwan mutane tserewa daga garin.

Kawo yanzu dai babu cikakken bayani kan irin asarar rayukan da aka yi sakamakon artabun.

Harin Gulak kuma na zuwa ne duka sa'o'i 24 da wasu da ake tunanin 'yan Boko Haram ne suka kashe kansu da wasu fararen hula biyu, a wani harin kunar bakin wake da suka kai a kusa da kan iyaka da Kamaru.

Wadannan hare-haren dai sun nuna har yanzu kungiyar Boko Haram barazana ce a yankin arewa maso gabashin Najeriya, duk da sojoji na ikirarin suna samun galaba a kan mayakan kungiyar.