Paradise Papers: Shin wa ya mallaki kulob din Everton?

Wayne Rooney and Alexis Sanchez Hakkin mallakar hoto PA/ Getty Images
Image caption Dokokin gasar Firimiya suna da tsauri dangane da mallakar kungiyoyin kwallon kafa

Takardun Paradise da aka bankwado sun nuna tababa kan asalin wanda ke tafiyar da kungiyar Everton, sannan ko kungiyar ta talauce.

Farhad Moshiri ya sayar da hannun jarinsa na Arsenal a 2016 domin sayen kaso 50 na Everton.

Amma bayanan kwarmaton sun nuna ya mallaki hannun jarin ne kamar kyauta daga attajirin Rasha Alisher Usmanov, wanda ke da kashi 30.4 na hannun jarin Arsenal, lamarin da wasu ke tababa ko yana da hannun jari a Everton.

Mista Moshiri ya musanta zargin cewa kudadensa na kyauta ne.

Lauyoyinsa a Everton sun musanta dukkanin zarge-zargen da ake game da saba dokokin gasar Premier.

Lauyoyin sun ce Moshiri attajiri ne kuma da kudadensa ya saka jari a kungiyar.

Lauyoyin da ke kare Usmanov sun ce akwai kura-kurai a zargin inda suka danganta binciken a matsayin kutse ga rayuwar wanda suke karewa.

Dokokin gasar Premier sun ce wanda ya mallaki kashi 10 na hannun jarin wata kungiya ba zai iya kuma mallakar wani kason hannun jarin wata ba, domin kaucewa ra'ayin da zai ci karo da bukatun kungiyoyin musamman a kan wasanninsu da kuma musayar 'yan wasa.

Bayanan sun ce Mista Usmanov da Mista Moshiri sun saye kashi 14.58 na hannun jarin Arsenal a 2007 tare ta hanyar wani kamfani da ake kira Red and White Holdings.

Kuma takardun Paradise da aka bankado sun ce kudaden da aka zuba domin sayen hannun jarin Arsenal sun fito ne daga wani kamfani da ake kira Epion Holdings mallakin Mista Usmanov, wanda aka ce a yanzu ya mallaki dala biliyan 15.8, kwatankwacin fam biliyan 12.

Daya daga cikin bayanan takardun sun ce "kudade daga Kamfanin Gallagher zuwa ga Alisher Usmanov wanda kuma zai bayar da kyauta ga Moshirri, wanda kuma zai ci gaba da saka jari a Kamfanin.

Kudaden Red and White sun fito ne daga kamfanin Epion Holdings limited.

Gallagher Holdings shi ma kamfanin Usmanov ne.

Amma tun da farko lauyoyin da ke kare Mista Moshiri sun musanta cewa kudaden sun fito ne daga Epion.

Daga baya kuma suka amsa cewa asalin kudaden sun fito ne daga Epion, amma suka ce Moshiri ya biya Usmanov daga baya.

Red and White Holdings ya ci gaba da rike hannun jarinsa a Arsenal da yanzu ya kai kashi 30.4

A watan Fabrairun 2016, Mista Moshiri ya sayar da rabin kason hannun jarinsa ga attajirin na Rasha.

Kuma Takardun Paradise daga Appleby, kamfanin da ke sa ido a yarjejeniyar, sun tabbatar da cinikin da aka yi domin samar da wasu kudaden sayen hannun jarin kulub din Everton, an ruwaito cewa kudaden cinikin sun kai fam miliyan 87.5.

Tun da farko dai wata kafar yada labaran Rasha da ke kusa da Mista Usmanov ce ta fara bada rahoton cewa "attajirin Rasha Alisher Usmanov ya zama sabon mai kungiyar Everton".

Amma nan take ne aka cire labarin, matakin da ya haifar da zargi.

Zargin dai ya kara girma a watan Janairu a lokacin da aka sanar da cewa Kamfanin Mista Usmanov ne ke daukar nauyin filin da 'yan wasan Everton ke atisaye, inda aka sauya filin da suna USM Finch Farm.

Lokacin da daya daga cikin 'yan jaridar BBC da ke gudanar da binciken ya tuntubi Mista Moshiri kuma ya tambaye shi cewa, ko Mista Usmanov ne ya mallaki Everton, sai ya kada baki ya ce: "Ba ka da hankali ne? Ka ga Likitan mahaukata ne?

Ya ce "Idan bashi ne, to kudi da zaka biya. Idan kyauta ce, to mallakinka ne. Amma duka ba ko daya domin na riga na biya."

Mista Moshiri ya ce dukkanin takardun da suka ambato cewa kyauta ce "to kuskure ne."

Lauyoyin Moshiri sun ce hukumomin Premier Lig sun gamsu bayan binciken da suka gudanar kan ko ya cika sharuddan mallakar kungiya.

Sannan sun ce Moshiri wanda Forbes ta ce ya mallaki kudi da suka kai dala miliyan 2.4 ya ci gaba da kula da hidimomin Everton da kudadensa.

Tsohon shugaban hukumar FA Greg Dyke ya shaidawa tawagar BBC da ke binciken cewa batun kyauta kamar almara ce, inda ya kara da cewa "idan har abin da takardun suka fada haka ne, to na tabbata Premier lig za ta gudanar da nata binciken".

Hakkin mallakar hoto VisMedia
Image caption Mista Moshiri ya ce dukkanin takardun da suka ambato cewa kyauta ce "to kuskure ne"

Sakamakon binciken zai dogara ne akan abin da mutanen biyu suka yi da kuma masaniyar da kugiyoyin ke da ita.

Da aka tuntube su kan batun, Hukumomin Premier sun ce ba za su iya cewa komi ba akan wata kungiya ko wasu mutane ba.

Kamfanin Bridgewaters ne ya jagoranci yarjejeniyar ta Everton.

Kuma wani bangare na takardun Paradise sun ce Mista Usmanov ya yo hayar kamfanin Bridgewaters ne a 2011 a sirrrance. Zargin da bangarorin biyu suka musanta.

Amma Blue Heaven Holdings, kamfanin da ke da mallakin Everton na da rijista ne a Bridgewaters kuma daraktocinsa guda biyu ma'aikatan Bridgewaters da ke aiki kuma a karkashin kamfanin Mista Usmanov, USM Holdings.


Wane ne Alisher Usmanov?

Hakkin mallakar hoto Getty Images
  • An haife shi ne a Uzbekistan a 1953, amma dan asalin Rasha ne
  • Ana masa lakabi da "Jarumin Rasha", ya samu arzikinsa a sana'ar robobi da ma'adinai da karafa
  • Daga baya ya fadada kasuwancinsa zuwa saka jari a kafofin sadarwa na zamani da wayoyin salula
  • Yana da hannun jari kashi 30.4 a Arsenal
  • Ya taba zama gidan kaso a 1980 zamanin daular Soviet kan badakalar sata da zamba, amma kotun kolin Uzbekistan ce ta wanke shi a 2000, tana mai cewa an kirkiri hujjojin ne.
  • Musulmi ne, kuma a 1992 ya auri Irina Viner wata mai bayar da horo a motsa jiki, kuma an ruwaito cewa makusanci ne ga Vladimir Putin.

Lauyan Mista Usmanov ya ce akwai kura-kurai kan bayanan zargin amma ba tare da ya yi karin haske ba.

A watan Mayu, Usmanov ya nemi karbe hannun jarin Stan Kroenke wanda ke da kaso mafi tsoka a Arsenal, matakin da zai ba shi damar mallakar kaso 96 na hannun jarin kudniyar.

Labarai masu alaka