Fursunoni mata na karuwa a duniya

Mata kan aikata laifukan da ke kai su zama a gidan yari Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mata kan aikata laifukan da ke kai su zama a gidan yari

Wani bincike da aka gudanar a kan yawan mata da 'yammatan da ke zaman gidan yari a sassan duniya daban-daban, ya gano cewa adadin matan ya karu musamman a shekarun baya-bayan nan.

Binciken ya kiyasta cewa yanzu haka akwai mata fiye da dubu dari bakwai da ke zaman gidan gidan kaso a duniya.

A cewar wata cibiyar da ke bincike kan manyan laifuka da ke birnin London, adadin matan da ke zaman gidan kaso na karuwa a kowacce nahiya a cikin shekaru 17 da suka wuce, kuma an fi samun karuwar adadin fursunoni mata ne a kasashen Brazil da Indonesia da Phillipines da kuma Turkiya.

Cibiyar ta ce, inda kuma ake da yawan fursunoni mata su ne Amurka da kuma China.

A shekarar 2015, China ta samu karuwar fursunoni mata da yawa wadanda suka aikata laifukan da suka hadar sa sarafar miyagun kwayoyi da kuma cin hanci inji cibiyar.

Hakan ya sa China ta zamo kasa ta biyu a duniya da ta ke da yawan fursunoni mata.

To amma duk da haka yawan fursunoni mata na China bai kai rabin fursunoni matan da ke Amurka ba.

Kuma wadannan fursunoni wasu na zaune ne kafin a yanke musu hukunci, yayinda wasu kuma ke zaman hukuncin da aka yanke musu.

Masu bincike sun ce ana kashe makudan kudade wajen kula da fursunoni mata, to amma duk da haka baya wani tasiri ko kadan idan sun dawo cikin al'umma.