Nigeria: Kotu ta wanke 'yan Shi'a a Kaduna

Shia Hakkin mallakar hoto Getty Images

Wata babbar kotu a Kaduna ta saki wasu daga cikin mabiya Shi'a da aka kama kuma aka gurfanar da su a gabanta sakamakon rikicin da ya faru tsakaninsu da sojojin Najeriya a watan Disamban 2015.

Mai shari'a Esther Lolo ce ta wanke 'yan Shi'ar guda 10 da aikata laifuffuka biyar da ake tuhumarsu.

Tun a shekarar 2016 aka gurfanar da mabiyan Shi'a a kotu kan laifuffuka da suka shafi shirya gangami ba kan ka'ida ba, da tayar da zaune tsaye da takurawa al'umma.

Kotun ta wanke su ne bayan wadanda suka shigar da karar sun gaza gabatar da wasu kwararar hujjoji kan zargin da ake wa 'yan Shi'ar ba.

Falana ya bukaci a saki Zakzaky

A ranar Laraba ne Lauyan da ke kare Jagoran kungiyar 'yan Shi'a a Najeriya (IMN), Ibrahim el-Zakzaky, ya bukaci mahukuntan kasar da su saki malamin saboda "tabarbarewar lafiyarsa," kamar yadda ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP.

Kimanin shekara biyu ke nan da ake tsare da malamin bayan rikicin da sojoji.

Lauyansa Femi Falana ya ce ya kamata Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya saki jagoran kungiyar bisa "dalilan lafiyarsa", kamar yadda ya bayyana a wata wasika da ya aike wa shugaban kasar ranar Laraba.

Ya ce malamin wanda ya rasa idonsa na dama yayin da ake kokarin kama shi, "yana cikin hadarin rasa idonsa na hagu," in ji shi.

Falana ya ce halin da mai dakinsa Zainab take ciki "ya fi muni" yayin da ya kai musu ziyara a wani wurin sirri da ake tsare da su a Abuja.

Labarai masu alaka