Germany: Ma'aikacin jinya ya hallaka marasa lafiya 100

Mr Niels Hoegel na ba wa marassa lafiya maganin da ya fi karfinsu ne don su farfado, amma kuma sai a samu akasi
Bayanan hoto,

Mr Niels Hoegel na ba wa marassa lafiya maganin da ya fi karfinsu ne don su farfado, amma kuma sai a samu akasi

Wani bincike da aka gudanar ya gano cewa wani tsohon ma'aikacin jinya a kasar Jamus ya hallaka akalla mutum 100 a asibitoci biyu da ya yi aiki.

Masu bincike sun ce Mr Niels Hoegel, wanda yanzu haka aka yanke masa hukuncin daurin rai da rai saboda kashe wasu mutum biyu, bayan ya yi amfani da wata dabara ta basu maganin ciwon zuciya fiye da kima.

Mr Hoegel, mutum ne mai son ya burge abokan aikinsa ta hanyar kokarin farfado da marassa lafiyar da ya ke jinya, inda a garin neman gira kuma sai ya rasa ido, saboda garin ya ceto su sai kuma yawancinsu su mutu saboda maganin da yake basu yafi karfin adadin da ya kamata a ba su.

Yanzu dai ana kyautata tsammanin za'a fara masa wata sabuwar tuhumar a shekara mai zuwa, saboda ana zargin ya kashe mutum kusan 100 a tsakanin shekarun 1999 da 2005 a wasu asibitoci biyu da ya yi aiki a arewacin Jamus.

Masu bincike ma sun ce akwai yi wuwar ya kashe mutane fiye da haka saboda ana tunani cewa idan ya kashe wasu marassa lafiyar da ba a fargaba ma kona su yake.

Idan har aka same shi da laifin wannan kisan inji masu binciken, to zai zamo daya daga cikin mutanen kasar Jamus ya kashe mutane da dama.

Masu bincike sun gano cewa anfi samun mace-mace a asibitocin biyun da ya yi aiki a duk lokacin da Mr Hoegel din ke aiki.

Dubunsa ta cika ne bayan da wata ma'aikaciyar jinya ta fuskanci cewa wata marar lafiya na cikin hayyacinta amma daga bisani bayan ya shiga dakin da ta ke kwance sai ta fara samun matsalar bugun zuciya, daga nan sai ma'aikaciyar jinyar ta duba maganin da ke teburin marar lafiyar taga ba bu komai sai kwali a bola.

A lokacin da ake yanke masa hukunci na farko ya ce idan yaga mutum ya mutu ta sanadiyyar bashi magani fiye da kimar da ya yi, ya kanyi nadama ya ce ba zai kara ba, amma kuma daga baya sai kuma yaga cewa ai shifa sai ya burge abokan aikinsa don haka sai ya yi kokarin farfado da marar lafiyar da ya ke kula dashi ta hanyar bashi maganin d yafi karfinsa musamma ga masu ciwon zuciya.