Hotunan abin da ya faru a Nigeria a makon jiya

Hotunan wasu daga cikin manyan abubuwan da suka faru a sassa Najeriya daban-daban a makon jiya.

Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Bukola Saraki yayin da sabon Sakataren Gwamnatin Najeriya Boss Mustapha ya kai masa ziyara a ofishinsa ranar Litinin

Asalin hoton, Nigeria Presidency

Bayanan hoto,

Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Bukola Saraki yayin da sabon Sakataren Gwamnatin Najeriya Boss Mustapha ya kai masa ziyara a ofishinsa ranar Litinin

Asalin hoton, NITDA

Bayanan hoto,

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da Shugaban hukumar bunkasa fasahar zamani, Sheikh Isa Pantami, yayin bikin bude wani taro kan fasahar zamani a Abuja ranar Talata

Asalin hoton, DG Media

Bayanan hoto,

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje yayin da za a kona jabun magunguna a harabar ofishin hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) a Kano ranar Litinin.

Asalin hoton, Nigeria Presidency

Bayanan hoto,

Shugaban Ma'aikatan Shugaban Najeriya, Abba Kyari, tare da Shugabar Ma'aikatan Gwamnatin Najeriya, Winifred Oyo-Ita, lokacin taron majalisar zartarwar a fadar shugaban kasa da ke Abuja ranar Laraba

Asalin hoton, Nigeria Presidency

Bayanan hoto,

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayin da yake gabatar da kasafin kudin shekarar 2018 a zauren majalisar dokokin kasar ranar Talata

Asalin hoton, Nigeria Presidency

Bayanan hoto,

Jana'izar uwargidan Sanata Danjuma Goje, Hajiya Yalwa, wadda aka yi wa sallah a fadar sarkin Gombe a jihar Gombe, ranar Alhamis. Marigayiyar ta rasu ne a kasar Amurka a karshen watan jiya.

Asalin hoton, Nigeria Presidency

Bayanan hoto,

Uwargidan Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, Aisha, yayin da ta je ta'aziyyar rasuwar uwargidan Sanata Danjuma Goje, Hajiya Yalwa, a Gombe ranar Juma'a

Asalin hoton, DG Media

Bayanan hoto,

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje yayin bikin kaddamar da wani shirin tallafawa matan jihar a filin wasa na Sani Abacha da ke Kano ranar Alhamis

Asalin hoton, Imo State Government

Bayanan hoto,

Shugabar kasar Laberiya Ellen Johnson Sirleaf tare da gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha lokacin da ta kai ziyara jihar ranar Juma'a

Asalin hoton, Nigeria Presidency

Bayanan hoto,

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari bayan ya gana da mambobin kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) a fadarsa da ke Abuja ranar Juma'a

Asalin hoton, Nigeria Presidency

Bayanan hoto,

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da Shugaban kungiyar Jama'atu Izalatu Bidi'a Wa'iqamati Sunna (JIBWIS), Sheikh Abdullahi Bala-Lau, a fadarsa da ke Abuja ranar Juma'a

Asalin hoton, Nigeria Presidency

Bayanan hoto,

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari bayan ya gana da malaman addinin Musulunci a fadarsa da ke Abuja ranar Juma'a

Asalin hoton, DG Media

Bayanan hoto,

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje a teburin mai shayi lokacin kaddamar da tallafa wa matasa fiye da 5,000 don fara sana’ar shayi a Kano ranar Asabar

Asalin hoton, Sani Ballack

Bayanan hoto,

Wani bangare na kasuwar garin Nguru da ke jihar Yobe, inda gobara ta cinye shaguna a safiyar ranar Asabar