Girgizar kasa ta kashe mutum 330 a Iran da Iraq

Iran Iraq Hakkin mallakar hoto REUTERS/TASNIM NEWS AGENCY
Image caption Girgizar kasar ta auku ne a lokacin da mutane da yawa ke cikin gidajensu

A kalla mutum 330 ne suka mutu a Iran bayan wata kakkarfar girgizar kasa ta auka cikin wani yankin tsaunuka a kan iyakarta da Iraki.

Wata hukumar bayar da agaji ta Iran ta ce mutum 70,000 na bukatar mafaka bayan afkuwar girgizar kasar, wadda daya ce daga cikin manyan da suka faru a wannan shekarar.

A kalla mutum 207 daga cikin wadanda suka rasu din suna lardin yammaci na Kermanshah ne, yayin da girgizar kasar ta kashe wasu mutum bakwai a wasu wurare a Iran din.

Kazalika mutum bakwai sun mutu a Iraki yayin da mutane suka tsere cikin babban birnin kasar, Bagadaza.

Jami'an Iran sun ce fiye da mutum 1,600 ne suka ji raunuka.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wani kanti kenan da girgizar kasar ta shafa a kusa da yankin Halabja inda iftila'in ya fi tsanani

Tsagewar da kasa ta yi ya kutsa har cikin iyakar Iraki kusa da birnin Kurdawa na Halabja, abin da ya janyo mutuwar mutum shida zuwa yanzu.

Gine-gine sun ruguzo kuma lantarki ya katse yayin da zaftarewar kasa ke kawo tsaiko ga ayyukan ceto.

An fahimci cewa babban asibitin da ke garin Sarpol-e-Zahab ya rushe gaba daya.

Akwai kuma wasu rahotanni da ke cewa wani asibiti a cikin Iraki ko kuma a kan iyaka cikin yankin Kurdawa mai kwarya-kwaryan 'yanci ya lalace.

Haka kuma, kasashe kamarsu Israila da Kuwaiti duk sun ji rugugin wannan girgizar kasa.

Hakkin mallakar hoto REUTERS/TASNIM NEWS AGENCY
Image caption Ana tsammanin yawan wadanda suka mutu a girgizar kasar ya karu

Labarai masu alaka