Amurka ta fara binciken kashe sojojinta a Nijar

Nigerien Army Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Sojojin Nijar na samun horo da sauran tallafi daga takwarorinsu na Amurka

Masu bincike daga Amurka da kuma jamhuriyar Nijar sun kai ziyara yankin da wasu masu ikirarin jihadi suka far wa sojojin kasashen har ta kai ga kashe hudu cikin dakarun kowaccensu.

Sojojin Amurka sun ce ayarin binciken ya zanta da mutanen kauyen Tongo Tongo a yammacin Nijar a kokarin gano takamaimai abin da ya faru.

Harin ya zama wani babban al'amari cikin siyasar Amurka saboda mutuwar dakarun kasar.

Amurka ta ce ziyarar wani bangare ne na binciken hukumomin kasar masu yawa da zai shafi nahiya uku.

Maharan wadanda ake kyautata zaton sun shiga kasar daga makwabciyarta Mali sun yi wa dakarun Nijar da na Amurka kwanton-bauna a Tongo Tongo da ke arewacin jihar Tillabery, inda suka kashe sojin Amurka hudu da na Nijar hudu.

Rahotanni an yi wa dakarun hadin gwiwar kwanton bauna ne yayin wata raraka da suka yi wa 'yan ta-da-kayar-bayan.

Sojojin Amurka na ba da horo da sauran taimako ga takwarorinsu na Nijar domin taimaka wa yaki da mayaka masu ikirarin jihadi, wadanda suka hada da reshen kungiyar Al Qaeda na Arewacin Afirka.