Ba zan yi watsi da al'ummar Igbo ba - Buhari

Shugaba Buhari a jihar Ebonyi Hakkin mallakar hoto Nigeria Presidency
Image caption An karrama Shugaba Buhari da kayayyakin gargajiya na Igbo

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ba zai yi watsi da al'ummar Igbo da ke kudu maso gabashin kasar a duk tsawon mulkinsa.

Da ya ke magana a lokacin da ziyarar da ya kai yankin, shugaban ya ce zai cika dukkan alkawuran da ya daukar wa jama'ar yankin.

"Kamar yadda na fada a baya... Ina sake jaddada wa cewa ba zan yi watsi da ku ba". Ya kara da cewa "Najeriya kasarmu ce mu duka".

Al'ummar yankin dai sun sha zargin gwamnatin shugaban da nuna musu banbanci, lamarin da jami'ai suka sha musanta wa.

Wannan ce ziyara ta farko da Shugaba Buhari ya kai yankin tun bayan hawansa mulki. Kuma ta zo ne duk da barazanar da kungiyar fafutikar kafa kasar Biafra ta IPOB ta yi masa na tayar da tarzoma a lokacin ziyarar.

An dai tsaurara matakan tsaro a jihohin Ebonyi da Enugu da ya ziyarta, kuma kawo yanzu babu wani labarin tashin hankali.

A ranar Laraba ne ake sa ran shugaban zai ziyarci jihar Anambra inda zai halarci taron yakin neman zabe na dan takarar gwamna na jam'iyyarsa ta APC.

Wasu dai na cewa Shugaba Buhari ya ziyarci yankin ne domin halartar taron yakin neman zaben, amma makusantansa sun musanta.

Ra'ayoyin jamar yankin dai sun sha bambam kan wannan ziyara, inda wasu ke maraba da ita, yayin da wasu kuma cewa shugaban ya yi latti.

Hakkin mallakar hoto Nigerian Presidency
Image caption Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da ayyukan ci gaban kasa a yankin

Akasarin mutanen da BBC ta zanta da su ta wayar tarho sun ce suna wa Shugaba Muhammadu Buhari maraba a wannan ziyara ta farko da zai kai yankin.

Wasu Igbo dai sun sha sukar Muhammadu Buhari kan yadda suka ce ba ya damawa da al'ummar yankin a gwamnatinsa.

Al'amarin da ya zafafa rajin ballewa daga Najeriya a tsakanin wasu matasan yanki a baya-bayan nan.

Sai dai, wani Igbo ya ce: "Za mu yi masa marhabin ta yadda zai yi wa yankinsu wani aikin ci gaban kasa. Ai Najeriya kasarmu ce."

Za mu yi murna da zuwansa, in ji shi.

Ita ma wata ta ce "Ai babu damuwa! Ina farin ciki da haka. Ziyarar za ta sa mu ji cewa Najeriya daya ce babu batun nuna bambanci tsakanin Bahaushe ko Bayarabe ko Igbo."

Ta ce wato dukkan al'ummar kasar daya suke. "Ina kaunar wannan ziyara da Buhari da zai kawo yankinmu".

Haka zalika, mutanen yankin na Kudu Maso Gabas na zargin gwamnatin Buhari da rashin gudanar da ayyukan raya kasa, inda suka ce yana nuna fifiko a mulkinsa.

Shi kuma wani tsohon dan jarida a yankin, Kalu Ezee na cewa da ma ya kamata Buhari ya kai wannan ziyara.

A cewarsa tun da aka kammala zabe, Buhari bai samu damar ziyartar yankin ba, don haka zuwansa zai magance wasu abubuwa da dama.

"Ka san mutanenmu kafin ya zo, suna gani kamar bai yi musu wasu ayyukan alheri sosai ba, don haka wannan dama ce gare shi ya fada musu abubuwan da ke zuciyarsa," in ji Mista Kalu.

Hakkin mallakar hoto Nigeria Presidency
Image caption Gwamnonin yankin da dama sun hallara domin tarbar shugaban

Ya ce mutanen yankin su ma za su samu damar yi masa bayani game da matsalolin da suke ci wa al'ummar yankin tuwo a kwarya.

A cewarsa: "Za su yi masa magana a kan (mawuyacin hali da) hanyoyin gwamnatin tarayya da ke yanki. Za su yi magana a kan (aikin) gadar Neja ta biyu, wato gadar nan ta Onacha, ka san ta dade ana maganarta."

Dan jaridar ya ce al'ummar yankin za su so su bijirowa da Shugaba Buhari batun samar da ayyukan yi ga matasa da kuma tsaro.

"Za su yi magana game da rikicin nan da ke faruwa tsakanin manoma da makiyaya, Mista Kalu ya ce.

An tambaye shi ko za a bijiro wa shugaban maganar kafa kasar Biafra sai ya ce: "Maganar Biafra ba za ta taso ba, don kuwa kungiyar Ohaneze Ndigbo ta rika ta magance al'amarin".

Labarai masu alaka