An yi karar ministan ilimi kan fadawar yaro shaddar gargajiya

bandaki a Afirka Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Al'ummomi da dama a Afirka na fama da rashin bandaki

Wata kafar yada labaran intanet ta Times Live a Afirka Ta Kudu ta ce, iyayen wani yaro sun shigar da karar ministan ilimi na Afirka Ta Kudu Angie Motshekga, bayan da dansu ya fada cikin shaddar gargajiya.

Kafar yada labaran News 24 ta ruwaito cewa a shekarar 2014 ne Michael Komape ya fada cikin wata shaddar gargajiya a makarantar firamare ta Mahlodumela da ke Limpopo, ya kuma nutse a cikin kashin mutane, wanda ya yi sanadin mutuwarsa.

Iyayensa sun ce shaddar ta lalace ne ta yadda bai kyautu a bar mutane su dinga amfani da ita ba, don haka suke bukatar dala 207,000 a matsayin diyya.

A ranar Litinin ne aka fara gudanar da shari'ar a babbar kotun da ke Polokwane.

Sashen ilimi a matakin farko na kasar ya gabatar da bayaninsa ga kotun inda yake watsi da batun cewa ministan ilimi ne ya jawo mutuwar yaron.

Labarai masu alaka