Russia 2018: Italiya ta gamu da 'babban bala'i'

Italy vs Sweden Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Tun farko Sweden ta ci kasar Italiya 1 - 0, sannan a wasan fitar da gwani kuma suka canjaras ba ci

Cikin kuka golan Italiya Gianluigi Buffon ya ba wa 'yan kasarsa hakuri, lokacin da ya yi ritaya daga taka leda, bayan sun gaza samun cancantar zuwa gasar Kofin Duniya.

Sweden ce ta rike wa Italiya wuya har suka tashi canjaras babu ci a birnin Milan, abin da ya hana wa kasar damar zuwa Rasha badi karon farko tun 1958.

Karo hudu a tarihi Italiya tana lashe gasar Cin Kofin Duniya.

Sakamakon dai na nufin kungiyar kwallon kafar Italiya ta Azzurri ba za ta halarci gasar ba a karo na biyu kenan cikin tarihi bayan ta ki taka rawa a farkon bude gasar Cin Kwallon Kafa na Duniya a 1930.

Dungurar wani da kwallon dan wasan tsakiyar Sweden Jakob Johansson ta yi kuma ta fada raga a karawar farko ta zama sanadin fitar da Italiya duk da wasan da suka yi zagaye na biyu a filin San Siro na birnin Milan inda aka tashi canjaras ba ci.

Sweden ta yi amfani da damar da ta samu kuma duk da rike kwallon da masu masaukin baki suka yi har kashi 75%, amma dai sun gaza yin wani gamon katar - Italiya ta samu babbar dama ta hannun Stephan El Shaarawy amma golan Sweden Robin Olsen ya sa hannu ya ture.

Sakamakon ya ba wa kungiyar Sweden ta Jan Andersson damar kai wa ga Gasar Kofin Duniya karon farko tun bayan shekara ta 2006.

Wata marubuciya kan harkar kwallon kafar Italiya, Mina Rzouki ta ce ra'ayoyin mutane sun sha bamban a kan wannan sakamako a kasar.

A cewarta: "Wasu a cikinmu na cewa akwai bukatar mu yi faduwar bakar tasa ta yadda za muke sake lale. Mu koma kan alkiblar da ta sa muka yi zarra tun da farko."

Wata babbar jaridar wasanni a Italiya mai suna La Gazzetta dello Sport ta kwatanta abin da ya faru da wani mummunan bala'i.

Ta kuma yi kira ga hukumomin kasar su kori kocin Italiya, Gian Piero Ventura.