Nigeria ta shigo da maganin maciji

A type of venomous snake found in Nigeria

Hukumomi a Najeriya sun ce sun sayo maganin dafin maciji, daga kasashen Birtaniya da Costa Rica bayan watanni ana fama da rashin maganin a asibitocin dake kula da masu fama da ciwon.

Fiye da mutum 200 sun rasa rayukansu a watan jiya daga sarar maciji saboda rashin maganin.

Yankunan da matsalar tafi kamari sun hada da Kaltungo dake jihar Gombe da Zamko dake jihar Filato, inda a kullum ake samun wadanda suka rasa rayukansu.

Jami'an kiwon lafiya sun ce an fara raba magungunan kimanin 5,000 ga cibiyoyin dake kula da wannan matsalar a cikin Najeriya.

Masana sun kiyasta cewa maciji na sarar fiye da mutum 10,000 a kowace shekara a Najeriya, kuma daruruwan mutane kan rasa rayukansu a sakamakon haka.

Saboda Najeriya bata iya samar da maganin macijin a cikin gida, ta kan aika da samfurin dafin macijin zuwa kasahen waje domin a hada maganin.