Ya kamata a mutunta kundin tsarin mulkin Zimbabwe - Buhari

Mugabe Hakkin mallakar hoto AFP

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi kira da a kwantar da hankali da zama lafiya da kuma mutunta kundin tsarin mulkin kasar Zimbabwe.

A wata sanarwa da mai ba shi shawara kan yada labarai Femi Adesina ya fitar, ya ce shugaban ya byi kira ga dukkan jam'iyyun siyasa da masu ruwa da tsaki a harkar soji da ke Zimbabwe da su guji yin duk wani abu da zai jefa kasar cikin rikicin da bai dace ba wanda kuma zai yi wa kasar da ma nahiyar illa.

A cewar Shugaba Buhari, "Dole ne a yi duk wani kokari don warware matsalolin da ake fuskanta ta hanyar bin kundin tsarin mulki na Zimbabwe don ceto kasar daga rikicin siyasa."

Wannan kira dai na shugaban Najeriyar na zuwa ne bayan da sojojin kasar Zimbabwe suka yi ikirarin cewa sun kwace mulki daga hannun farar hula, saboda yadda ake samun karuwar sa-in-sa kan sha'anin siyasa a kasar.

Sa-in-sar dai na faruwa ne bayan da Shugaba Robert Mugabe ta cire mataimakinsa Emmerson Mnangagwa daga mukaminsa.

Wannan a'amari ne ya jawo shugaban sojojin kasar General Constantino Chiwenga, ya yi barazanar cewa 'sojoji za su shiga cikin al'marin' tun da batu ne da ke da alaka da kare juyin-juya hali.

Labarai masu alaka