Kasar UAE na shirin fara noma abinci a duniyar Mars

Artist's impression of UAE's Mars domes Hakkin mallakar hoto Dubai Media Office
Image caption Yanzu kasar tana da wani babban buri - wato burin shuka bishiyoyin kwakwa da kuma ganyen latas a duniyar Mars

Wani abu da za a iya zargin Hadaddiyar Daular Larabawa da shi shi ne rashin kyakkyawan tsarin tunkarar gaba.

Da farko sun bayyana wani shirin da za su yi a duniyar Mars. Sannan kuma hakan ya yi arashi da burin karbe iko da duniyar.

Yanzu kasar tana da wani babban buri - wato burin shuka bishiyoyin kwakwa da kuma ganyen latas a duniyar Mars.

Bangaren binciken sararin samaniya ya kasance babban bangare ne a kasar, inda ake shirya manyan taruka kuma ake gayyatar manyan masana kimiyya kamar Al Worden, wanda ya taba zuwa duniyar wata a cikin kumbo Apollo 15.

Amma gabanin na'urar bincike ta UAE ta tashi zuwa duniyar Mars daga Japan a shekarar 2020, UAE din na aikin hadin gwiwa da babbar masana'anta ta Mitsubishi, inda a yanzu ta sanar da shirinta na fara aikin noma a can.

Wani babban jami'i na hukumar kula da sararin samaniyar kasar Rashid Al Zaabi, ya ce: "Akwai kamanceceniya sosai tsakanin duniyar Mars da hamada. Yanayin filin duniyar da kasar wajen iri daya ne."

Don haka UAE ta yanke shawarar zuba kudi a wasu ayyukan bincike biyu, noma bishiyoyin kwakwa da tumatur a duniyar Mars.

Mr Al Zaabi ya ce: "Ai idan muka je can dole muna bukatar cin abinci."

Hakkin mallakar hoto Dubai Media Office
Image caption A yanzu kuwa UAE na aiki ne wajen bunkasa fannonin kimiyya da fasahar zamani

An zabi shuka bishiyar kwakwa ne saboda yadda alamarta ke da alaka da yankin, sauran itatuwan kuma saboda masana kimiyya sun yarda cewa za su iya girma a duniyar Mars.

Duk da cewa wannan abun zai zama kamar tatsuniya, to akwai muhimman dalilan tattalin arziki da suka sa za mu yi.

Kasar UAE, musamman ma Dubai da Abu Dhabi, suna kokarin habaka tattalin arziki a shirye-shiryensu na kawo karshen zamanin amfani da kasa.

Kasar ta fara ne da gagarumin fadada bangaren yawon bude ido da harkokin jiragen sama, da kuma ayyukan fasaha da ke tattare da su.

A yanzu kuwa UAE na aiki ne wajen bunkasa fannonin kimiyya da fasahar zamani.

Shugaban aikin nomar da za a yi a duniyar Mars Omran Sharaf, ya ce: "Akwai matasa miliyan 100 da ke yankin kasashen Larabwa.

Hakkin mallakar hoto MBRSC
Image caption Kasar UAE dai ta sanya jarin fiye da dala biliyan 5.4 a bangaren hukumar sararin samaniyarta

"Muna so su taka rawa nan gaba wajen kai yankin matakin ci gaba.

(Yawan al'ummar UAE dai ya kai miliyan tara, wadanda daga cikinsu miliyan 1.4 ne kawai 'yan asalin kasar.)

Ya kara da cewa: "Ana magana ne a kan kirkirar wani yanayi bayan an daina dogaro, yanayi na dogaro da ilimi da kuma yanayin kirkirar wasu hanyoyin inganta tattalin arziki. Don haka yana da muhimmanci a samar da cibiyar kimiyya.

"Mun kirkiri injiniyoyi, amma ba masana kimiyya sosai. Wannan harka ta duniyar Mars kuwa aikin kimiyya ne zalla."

Kasar UAE dai ta sanya jarin fiye da dala biliyan 5.4 a bangaren hukumar sararin samaniyarta da suka hada da tauraron dan adam.

An kaddamar da wani gwaji na karshe da aka yi na bincike kan aikin da za a yi a duniyar Mars.

An samar da tauraron dan adam din binciken ta hanyar amfani da wata tawaga wadda ta hada zallar 'yan kasar Daular Larabawa, kuma za ta nemo inda ruwa yake da kuma yanayin sararin samaniya, in ji hukumar binciken sararin samaniyar.

Hakkin mallakar hoto Dubai Media Office
Image caption The plan is that scientists and researchers will live in the sealed facilities for a year

Kasar UAE ta kuma fara aiki kan birnnin kimiyya a duniyar Mars, wata cibiya da za a sadaukar da ita don koyar da yadda za a mallaki duniyar ta Mars.

Jerin ayyukan da za a yi a wajen, ya kai murabba'i miliyan biyu da za a iya rayuwa da kuma wuraren bincike, zai taimaka wajen binciken abinci da ruwa da sauran abubuwan bukatu.

Wannan aiki na duniyar Mars da UAE ke yi ya sa ta zama daya daga cikin kasashe tara da ke kokarin gano yada za su shiga duniyar.

Mista Sharaf ya ce: "Hakan na nufin zuba jarinmu a fannin ilimi da kimiyya da dakunan gwaje-gwaje da jami'o'i, zai zama gagarumi.

Kuma a cewar matukin jirgin da ya taba zuwa duniyar wata a cikin Kumbo Apollo 15, Al Worden, abun yana kuma bukatar hadin kan kasashen duniya.

Ya ji dadin wannan buri na UAE, da kuma nasarar da aka samu zuwa yanzu.

Amma ya kara da cewa: "Sai dai kalubalen fasaha da za a samu zai yi wa kasa daya yawa."

Hakkin mallakar hoto Dubai Airshow
Image caption Matukin jirgin da ya taba zuwa duniyar wata a cikin Kumbo Apollo 15, Al Worden, ya ce abun yana bukatar hadin kan kasashen duniya

Babban darakta janar na hukumar kula da sararin samaniya ta Mohammed Bin Rashid, Yousuf Hamad Al Shaibani, ya ce babban dalilin da ya sa za a yi amfani da sararin samaniya wajen yin wannan aiki, shi ne don a jawo hankalin kwararru na kasashen duniya don su zo su taka tasu rawar.

Ya ce: "Yin amfani da sararin samaniya don yin bikin da aka saba duk shekarar na taron sararin samaniya a wannan mako, babbar dama ce ta haduwa da manyan kamfanoni da cibiyoyin sararin samaniya na duniya, a kuma gina dangantaka mai inganci."

Ko masu mulkin kasar UAE ma sun bayyana wannan abu da ake kokarin yi a matsayin wani abu gagarumin abu da ba kowa ke iya yi ba.

A dauka cewa komai ya tafi yada ake so, mataki na karshe shi ne wata tawagar mutane cikin jirgi za ta sauka a duniyar Mars nan da shekara 100.

Ba zai taba yiwuwa ba. Amma dai a kalla kasar ta samar da wata al'umma ta masana kimiyya a yankin kasashen Larabawa - wadda ta koyi yada za a shuka kayan marmari da kayan itatuwa da yawa a duniyar Mars.

Labarai masu alaka

Karin bayani