'Ana cin zarafin' matan Afirka da ke aikin gida a kasashen Larabawa

Rothna Begum Hakkin mallakar hoto Rothna Begum

Wani rahoton da kungiyar kare hakkin dan Adam ta Human Rights Watch ta fitar ya ce, matan kasar Tanzaniya da ke aiki a kasashen Oman da Hadaddiyar Daular Larabawa na fuskantar fyade da azabtarwa da cin zarafi daga iyayen dakinsu.

Fiye da mata 50 da aka yi hira da su a yayin gudanar da binciken ya ce, iyayen dakinsu kan kwace musu fasfo kuma ana tursasa musu yin aiki na tsawon sa'o'i 15 zuwa 21 a ko wacce rana.

Sai dai ma'aikatar kwadago ta Oman ta karyata hakan.

Kusan rahotanni biyu daga cikin biyar na nuna ana samun cin zarafi da kuma yi musu fyade.

Gwamnatin Tanzaniya dai ba ta ce komai ba kan binciken, wanda ya yi zargin cewa ofisoshin jakadancin kasar ba sa wani abun a zo a gani don taimakawa matan.

Ga dai abin da uku daga cikin matan ke cewa, inda suka bayar da labaran da suka hada da na yadda ake cin zarafinsu. Amma suna iya daga muku hankali:

'An min barazana da ruwan asid'

Hakkin mallakar hoto Rothna Begum

Dotto ta shaida wa Human Rights Watch cewa ta sayar da gonarta da ta gada daga iyayenta don ta biya wani kamfanin shirya tafiye-tafiye da ke Dar es Salaam, kudi kimanin dala 76, daidai da naira 27360, don tafiya zuwa Oman a shekarar 2015.

Matar mai shekara 32 ta ce iyayen dakinta kan lakada mata duka, su tursasa ta yin aiki tsawon sa'a 20 a duk rana, babu hutu, kuma suna biyan ta dala 130 (N46800) maimakon dala 210 (N75600) da aka yi yarjejeniyar bata.

"Na fara samun matsalar tabin hankali saboda rashin abokan mu'amala na kwarai. Na kuma yi ta fama da ciwon kai, don har na zaci ma ko haukacewa zan yi," in ji ta.

A haka dai kuma sai aka fara cin zarafina.

"Ina cikin goge wata doguwar rigara abaya, sai ta kone. Uwar dakina ta yi fushi sosai, na yi koakrin nuna mata cewa ni 'yar adam ce mai kuskure. Amma sai ta ki saurara ta, sai ta fara dukana ta kuma watsa min ruwa a fuska.

"Ta cewa danta ya samo ruwan asid. Na gudu cikin daki na buya na rufe don kar su shiga cikik.

A lokacin da ta je ofisihin jakadancin Tanzaniya don neman taimako, sai aka kulle ta na tsawon wata shida.

Ta ce tana iya tuna wa a wancan lokacin a watan Mayun 2016, akwai kusan mutum 60 a wajen.

"Ba a barin mu mu fita waje. An kulle mu cikin daki da kuma kicin."

Ta ce bayan ta tsere ofishin jakadancin ne uwar dakinta ta bukaci sai an biya ta dala 1,560 a madadin asarar da aka ja mata.

Dotto ta ce jami'an ofishin jakadancin sun yi ta kokarin shawo kaita ta koma gidan da take aikin.

Sun ce min: "Idan ba ki ba da hadin kai ba fa za su kai ki gidan yari. Don haka ya rage naki."

"Na ce, "Ta ya ya zan iya biya? Aikin wata biyu kawai na yi inda ake biyana dala 130, to ya ya zan yi biya?"

Ta je kotu kamar sau shida don sauraron batun warware matsalar, inda ofishin jakadancin suka hada ta da wani tafinta don ta bayar da labarin irin bakar wahalar da ta sha.

"Ina da hujja. An yanke ni a bayana da madubi, kuma na zo da wata yagaggiyar riga da aka dake ni lokacin da nake sanye da ita."

A karshe dai uwar dakin nata ta yarda ta yi watsi da karar, amma fa sai da Dotto ta biya dala 260 kudin jirginta na komawa gida.

'Maigidan ne ya yi min fyade'

Atiya, wadda ta tafi Oman a watan Yunin 2015, ta ce iyayen dakinta sun kwace mata fasfo dinta da wayarta, suna kuma tilasata mata yin aiki na tsawon sa'o'i 21 ba hutu.

Ta shaida wa Human Rights Watch cewa ko abinci ba ta iya ci sai an ba ta izini kuma kullum sai an dake ta.

Bayan mako uku ne ta yi kokarin guduwa, amma uwar dakinta ta dawo da ita ta kuma ce mata: "Idan kina son komawa dole sai kin biya mu kudin da muka kashe wajen daukoki, kusan dala 890, (N320400).

Kamfanin da ya yi jigilarta tafiyarta a Oman ya ce ba zai iya taimakawa ba.

A watan Afrilun 2016 sai da aka kai ta asibiti bayan da ta suma saboda yadda ba ta iya cin abinci sakamakon ciwon makogoro.

Bayan ta koma gidan kuwa, ta ce sai da iyayen dakinta suka dauki fansa.

"Matar ta fara dukana tana cewa: 'Ba wai kin dawo nan ba ne don ki sake rashin lafiya.'

"Ta kira kanwar mijinta don ta taimaka mata, suka yi min tsirara suka min duka da abun sakale kaya na roba.

"Masu aikin gini daga waje na jiyo ni ina ihu amma ba za su iya kawo min dauki ba.

"A lokacin da mijin ya dawo sai ya dauke ni ya kai ni daki ya min fyade, kuma ta baya ya neme ni. Bayan ya gama, sai washe gari suka sa ni a jirgi don komawa Tanzaniya.

"Suka kwace duk kudin da na samu, fasfo dina kawai suka bai. Suka kuma watsar da ni a filin jirgi kawai."

Ta kai rahoton duka da fyaden da aka yi mata ga 'yan sandan Tanzaniya da kuma sakatariyar masu hana fasa-kwabrin mutane da ma'aikatar cikin gida - na kai musu har da hotunan tabon dukan da aka yi min a baya.

Sai jami'an suka ce mata ai da tun a Oman din ta kai kara.

'Yan sanda dai sun kama wanda ya yi silar tafiyarta a Tanzaniya, amma ba ta gasmu da wannan hukunci ba kadai.

"Har yanzu ina jin takaici idan na tuna abun da ya faru dani. Kawai ina son a biya ni diyyar abun da aka yi min ne kuma a dawo min da hakkokin, albashina da kayana da wayata."

'An mayar da ni wajen masu cin zarafina'

Hakkin mallakar hoto Rothna Begum

Mwajuma ta ce ta tsere zuwa ofishin jakadancin Tanzaniya da ke Oman a shekarar 2015, bayan da iyayen gidanta suka ci zarafinta kuma suka hana ta albashin wata shida.

Ofishin jakadancin ya gaya mata cewa ba abun da za su iya yi sai dai wanda ya yi mata hanyar aikin ya karbe ta.

Mwajuma mai shekara 27 ta ce ba ta son komawa hukumar don kuwa ta ga yadda wanda ya kawo su aikin ke dukan mata a zuwan da ta yi a baya.

Don haka sai ofishin jakadancin ya samu tabbaci daga hukumar cewa za su mayar da ita gida. Amma maimakon haka sai aka tursasa ta ta yi aiki a wani sabon wajen da ta biya kudaden da aka yi wahalarta.

"A yayin da na ga wasu matan ana dukansu a can, sai na tsorata, sai matan suka ba ni shawarar cewa gara na yarda ko ni ma a dake ni. Sai tsoro ya sa na ce, to.

An dauki tsawon wata biyu ba a biyanta albashi, a wasu gidaje biyu da ta yi aiki.

Sun ce wai suna bai w wanda ya akwo ta ne.

Ta kai kukanta ga ma'aikatar cikin gida ta Oman, amma sai wanda ya kai su kasar ya ki halartar sauraron koarfin, amma daga baya ya mayar mata fasfo dinta.

Ta kai korafin cin zarafin da aka yi mata bayan ta koma Tanzaniya, amma kuma tana ganin ba a bi mata hakkinta yadda ya kamata ba.

"Ina jin takaici idan na ga mutane na tafiya Oman. Har sai da na je hukumar hana fasa-kwabrin mutane na kai karar abu da aka yi min.

"Sun ce, matsalar daga wajenku take, da ku ke nacewa sai kun je."

Labarai masu alaka