Amsar tambayoyinku kan masarautar Sarkin Musulmin Nigeria

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Bayanin Magajin Gari kan masarautar Sakkwato

Latsa alamar lasifikar da ke sama don sauraron wani dan bayani kan masarautar Sakkwato daga bakin Magajin Gari Hassan Danbaba:

Daular Usmaniyya a Sakkwato, babbar Daula ce mai zaman kanta a yammacin Afirka da aka kafa fiye da shekara 200, inda ake danganta Sarkin Daular a matsayin Sarkin al'ummar Musulmi a Najeriya.

BBC ta duba tarihin Daular Usmaniyya tare da tattaunawa da Masanin tarihi Kwamred Bello N Junaidu, da Magajin Garin Sakkwato, Alhaji Hassan Danbaba, wadanda suka amsa wasu tambayoyi da masu saurare suka aiko.

Dangantakar Masarautar Sokoto da Addinin Musulunci ita ce tambayar da ta fi yawa daga wajen jama'a

Kwamred Bello N Junaidu ya amsa ta.

Alakar masarautar Sokoto da addinin Musulunci ta samo asali ne saboda Mujaddadi Shehu Dan Fodiyo, a lokacin da aka yi masa mubaya'a bayan Musulmi sun yi hijira daga garin Degel zuwa Gudu a shekara ta 1804 a cikin watan Fabrairu saboda tsanancin mulkin Sarkin Gobir na wancan lokacin, (Shekaru sama da 200 da suka gabata).

Ya ce: "Don haka za a iya cewa Musulunci ne ya kafa Daular Sokoto sanadiyar Shehu Usman Dan Fodiyo bayan an yi jihadi, amma masana tarihi sun ce tun kafin zamaninsa, an yi sarakuna na musulunci amma a kasashen Hausa.

"Don haka Musulunci ne ya kafa daular ba sarauta ba.

"Bayan da Musulmi suka yi hijira ne zuwa Degel , sai suka zauna suka tattauna suka ga ya dace su zabi shugaba ko Jagora.

Hakkin mallakar hoto WhatsApp
Image caption Marigayi Sultan Sir Abubakar III wanda ya fi dadewa a tarihin masarautar

"To anan ne suka ga ya dace Shehu Usman Danfodiyo ya zama shugaba ko Amirul Muminin ko kamar yadda ake cewa da Fulatanci "Lamido Julbe".

"A lokacin an ce Dan Fodiyo ya ki amincewa da bukatar, sai da aka dauki lokaci sannan ya amince ya zama Sarkin Musulmi amma da sharadin cewa zai yi rawani amma da Qur'ani da Hadisin Manzo (SAW).

"A kan haka ne ya amince a yi masa mubaya'a amma da Al Qur'ani da Hadisi, kuma daga lokacin ne aka fara kiran Shehu Usman Danfodiyo Sarkin Musulmi.

"Daga nan ne Sarautar Sarkin Musulmi ta samo asali, duk wanda aka nada to ya zama Khalifan Danfodiyo."

Me ya sa Sakkwatawa ke rantsuwa da Rawanin Dan Fodio? Wannan ma wata tambaya ce da wasu daga cikin masu ziyartar shafin BBC suka aiko.

Kwamred Junaidu ya ce:

"Don Rawanin Sarkin Musulmi", "Don darajar Rawanin Dan Fodiyo", wadannan nan su ne ire-iren rantsuwar da wasu Sakkwatawa ke yi, ba wai don rawanin ba sai don Qur'ani da Hadisi da rawanin ya dogara a gare su.

Don haka idan Basakkwace ya ce "Don rawanin Sarkin Musulmi", yana nufin don "darajar Qur'ani da Hadisi," in ji Kwamred Junaidu.

Hakkin mallakar hoto WhatsApp
Image caption Sultan Muhammad Saad wanda shi ne Sarkin Musulmi mai ci tare da Sarkin Zazzau Dokta Shehu Idris

Tsarin Sarautar Sakkwato kafin Danfodiyo

Kafin Shehu Usman Danfodio, Sokoto na karkashin rikon mulkin Gobir ne kuma a wancan lokacin ana mulki ne na Sarauta, wanda kuma ba bisa tsarin Shari'ar Musulunci ba, mulki ne na gado daga kaka da kakanni.

Mulki ne na gargajiya kafin zuwan Mujaddadi Shehu Usman Danfodiyo.

An samu sauyi lokacin da musulmi suka yi wa Danfodiyo Mubaya'a, tun kafin ma a fara jihadi inda aka jaddada musulunci a kasashen Hausa 10 irin su Zazzau da Kano da Bauchi da aka bai wa tuta, dukkaninsu kuma suka dawo karkashin daular Sakkwato.

A ina Danfodio ya fara kafa Tuta?

A yankin Gudu a jihar Sakkwato, a nan ne Shehu Usman Dandofio ya fara kafa tuta inda musulmi suka yi masa mubaya'a bayan ya yi hijira daga mulkin Gobir.

A lokacin ma an ji Danfodiyo na cewa "Gudu yau ba Gudu", wato an kai iyaka, za a tsaya ba wani gudu domin kare addinin Musulunci.

Masana tarihi sun ce, musulmi sun ci gaba da yin kaura zuwa garin Gudu saboda Danfodiyo, kuma a nan ne aka kaddamar da Jihadi.

Masarautu nawa Danfodiyo ya ci da yaki?

Masarautu da dama ne Shehu Usman Danfodiyo ya ci da yaki, tun daga Najeriya zuwa Nijar da Burkina Faso da Jamhuriyar Benin.

A Najeriya Daulolin da Danfodiyo ya ci da yaki sun kai 18.

Kuma ya fara ne tun daga yankin Sokoto, kamar Sarkin Kabbin Yabo Muhammadu Mauje da aka ba tuta har zuwa Zamfara da 'Yan doto da Katsina da Adamawa da Ilori da Nupe da Bauchi.

Akwai kuma Jama'are da Misau da Hadeja da Kazaure, duk wadannan ne wurare ne da Danfodiyo ya jaddada addinin musulunci, kuma aka samu sauyi aka kafa masarautu na addini.

Hakkin mallakar hoto WhatsApp
Image caption Sultan Muhammad Maccido tare da Sarkin Argungu

Khalifa na Farko bayan rasuwar Danfodiyo

Sarkin Musulmi Muhammadu Bello, shi ne Khalifa na farko bayan rasuwar Shehu Usman Danfodiyo, wanda dansa ne da ya yi shugabanci bayan mahaifinsa, a tsawon shekaru 20, daga 1817 zuwa 1837.

Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ya ci gaba da shugabanci irin tsari na mahaifinsa Shehu Usman Danfodiyo domin jaddada dorewar Daular Usmaniya.

A zamaninsa ne aka yi yakin Gobirawa da Zamfarawa da suka kawo wa Sakkwato hari, amma duka ya ci su da yaki domin kare Daular Usmaniya.

Shin gidan Sarautar Sarkin Musulmi kashi nawa ya rabu?

Gidan Sarautar Sarkin Musulmi a Sokoto ya kasu ne gida biyar, wato 'ya'yan Shehu Usman Danfodiyo.

Gidan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello

Akwai gidan Sarkin Musulmi Abubakar Atiku Mai Katuru wanda Kabarinsa ke Katuru a cikin yankin Shinkafi cikin Jihar Zamfara.

Gidan Amadu Rufa'i wanda zuriyarsa ke Silame da Gidan Muhammadu Buhari wanda zuriyarsa ke rike da garin Tambuwal da Dogon Daji da Sifawa.

Sai Isa Autan Shehu, wanda shi ne na karshe daga cikin 'ya'yan Shehu Usman Danfodiyo maza guda 20, kuma zuriyarsa ce ke rike da garin Kware.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wasu kalamai da Shehu Danfodiyo ya taba yi a kan shugabanci

Dukkanin wadannan gidajen idan Sarautar Sarkin Musulmi ta fadi suna iya nema.

Gidan da bai taba Sarautar Sarkin Musulmi ba?

Sarautar Sarkin Musulmi ba ta taba fadawa ba a Gidan Amadu Rufa'i Dan Shehu, Sarkin Musulmi na bakwai. Kuma tun lokacin da Allah ya yi masa rasuwa a 1873, zuriyarsa ba su sake karbar Sarautar Sarkin Musulmi ba.

Haka ma gidan Isa Autan Shehu bai taba rike Sarautar Sarkin Musulmi ba. Amma 'ya'ya da jikokin gidan Bello da Atiku dukkaninsu sun yi Sarautar Sarkin Musulmi.

Wane Sarkin Musulmi ne ya fi dadewa?

Marigayi Abubakar na III, Sarkin Musulmi na 17 ne ya fi dadewa a Daular Usmaniya, wanda ya shafe shekaru 50 yana shugabanci, daga 1938 zuwa 1988.

Abubakar na III jika ne ga Mu'azu Sarkin Musulmi na tara, daga Sarkin Musulmi na biyu Muhammadu Bello.

Abubakar na III shi ne mahaifi ga Sarkin Musulmi mai rasuwa Muhammadu Maccido da Sarki na yanzu Sa'ad Abubakar na III.

Shin da gaske ne Ibrahim Dasuki dan Mace ne?

Ibrahim Dasuki ne Sarkin Musulmi na 18, wanda shugaban mulkin Soja a Najeriya Ibrahim Badamasi Babangida ya nada bayan rasuwar Abubakar na III.

A lokacin an yi hatsaniya a Sakkwato inda har wasu ke danganta Ibrahim Dasuki a matsayin dan mace da bai cancanta ya zama Sarki ba.

Amma Ibrahim Dasuki ya fito ne daga Gidan Muhammadu Rufa'i dan Shehu Usman Danfodiyo.

Halliru ne mahaifin Dasuki, shi kuma dan Abdullahi Bara'u, shi kuma dan Muhammadu Buhari, shi kuma dan Usman Danfodiyo.

Zuriyarsu Dasuki ne suka kafa garin Tambuwal da Dogon Daji da Sifawa.

Dangantakar Sarkin Musulmi da Masarautar Maradun

Gidan Sarautar Maradun gidan Muhammadu Bello ne, Sarkin Musulmi na biyu bayan Shehu Usman Danfodiyo.

Mu'alledi dan Sarki Muhammadu Bello ne ya kafa Masarautar Maradun.

Kuma Gidan Sarautar Maradun iya neman Sarautar Sarkin Musulmi.

Sai dai kuma watakila yanzu da aka raba Zamfara daga jihar Sakkwato, yana da wahala a samu wani daga Gidan Sarautar Maradun a matsayin Sarkin Musulmi, kamar misalin Gidan Sarkin Kontagora a jihar Neja wanda 'yan gidan Sarkin Musulmi Atiku ne.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Bayanin Magajin Garin Sakkwato kan sarautarsa

Latsa alamar lasifikar da ke sama don sauraron wani dan bayani kan sarautar Magajin Garin Sakkwato daga bakin Alhaji Hassan Danbaba:

Ko akwai Yarima mai jiran Gado a Sakkwato - Jama'a da dama sun yi wannan tambayar duk da cewa ba su saka sunayensu ba

Magajin Gari Alhaji Hassan Danbaba ya amasa tambayar da cewa: "Babu Yarima Mai jiran Gado a tsarin Masarautar Sarkin Musulmi.

"Idan har Sarauta ta fadi, manyan sarakunan Majalisar Sarki ke zaunawa su zabo sunaye daga gidajen gidan Shehu Usman Danfodiyo."

Su wa ke zaben Sarkin Musulmi?

"Wadanda ke da alhakin zaben sabon Sarkin Musulmi guda 11 ne da ake kira Sarakunan Karaga. Kuma cikinsu babu wani wanda kai-tsaye dan uwa ne ga Danfodiyo.

Sarakunan sun hada da:

1.Wazirin Sakkwato

2.Magajin Garin Sakkwato

3.Magajin Rafin Sakkwato

4.Galadiman Gari

5.Sarkin Yakin Binji

6.Sarkin Kabin Yabo

7.Ardon Dingyadi

8.Baraden Wamakko

9.Ardon Shuni

10.Sa'in Kilgore

11.Sarkin Adar na Dundaye

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Sarkin Musulmi Muhammadu Maccido ya rasu ne a shekarar 2006 sanadiyyar hatsarin jirgin sama

"A duk lokacin da Sarauta ta fadi su suke zaunawa su zabi sabon Sarkin Musulmi," in ji Magajin Gari Alhaji Hassan Danbaba.

Shin Zuriyar Danfodio kawai ake binnewa a Hubbare?

Kamar yadda Hubbare makaranta ce da mutane ke zuwa daukar karatu zamanin Usman Danfodiyo, haka za a iya rufe kowa a hubbaren saboda dangantakar Shehu Usman Danfodiyo da Addinin Musulunci.

Akwai kaburburan mutane da dama wadanda ba su da alaka da Danfodiyo illa ta addini.

Wasu da dama kan bar wasiyar neman alfarma a binne su a hubbaren Shehu, ba lalle sai zuriyar Mujaddadi ba.

Danfodiyo ya fadi abubuwa biyar a kan shugabanci.

1.Duk wanda ya nemi mulki ka da a ba shi domin ba zai yi adalci ba

2.Ba mulkin da zai dore idan ba a tuntubar jama'a

3.Shugaba bai gallazawa jama'a

4. Ana shugabanci da aikin kwarai

5.Shugabanci da Adalci.