'Da sake a kasafin kudin Niger na badi'

Shugaba Muhammadou Issufou na Jamhuriyar Nijar, na shan suka a kan kasafin kudin shekarar 2018 Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shugaba Muhammadou Issufou na Jamhuriyar Nijar, na shan suka a kan kasafin kudin shekarar 2018

A Jamhuriyar Nijar, kungiyoyin fararen hula ne suka fara taruka na wayar da kan al'umma bisa kasafin kudin 2018.

Hadin gwiwar kungiyoyin fararen hular, ya shaida wa jama'a cewa kashi 94 cikin 100 na kasafin kudin a jikin talaka za'a samo su, yayinda ake sa ran samun kashi uku cikin 100 na kudaden daga albarkacin ma'adinan da kasar ke da su.

Don haka ne gamayyar kungiyoyin ke ganin sam ba dai-dai bane, yakamata a samo wadannan kudade daga kamfanonin da ke kasar kamar kamfanin Uranium da Areva da kamfanin hakar zinare dama na hakar man fetur.

Kungiyoyin fararen hular sun ce, gudanar da tarukan ya zama dole saboda a sanar da jama'a irin yadda kamfanoni ke taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa tattalin arzikin kasa.

Kungiyoyin sun ce, ba za su zuba idanu suga gwamnati na yin abinda bai dace ba musamman ga al'ummar kasar domin daga karshe talaka ne zai sha wuya.

Don haka suka ce wannan kasafin kudi na badi, lallai akwai sake, dole ayi gyara.

Labarai masu alaka