Kalli hotunan zanga-zangar adawa da Mugabe

Ana ci gaba da matsa wa Shugaba Robert Mugaba lamba kan ya sauka daga kan mulki biyo bayan kifar da gwamnatinsa da sojoji suka yi ranar Laraba.

Masu zanga-zanga

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Masu zanga-zanga sun nufi fadar Shugaban Zimbabwe Shugaba Robert Mugabe don su bayyana bukatarsu ta shugaban ya sauka daga mulki.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Gangamin ya samu goyon bayan rundunar sojin kasar wadda ta kifar da gwamnatin kasar a ranar Laraba

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Sojojin Zimbabwe sun yi wa Mista Mugabe daurin talala a birnin kasar Harare ranar Laraba

Bayanan hoto,

Kimanin shekara 37 ke nan da Mista Mugabe yake mulkin kasar

Bayanan hoto,

A farkon watan nan ne Mugabe ya kori mataimakinsa, Emmerson Mnangagwa, wanda ake ganin yana samun goyon bayan rundunar sojin kasar a halin yanzu

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Sai dai mataimakin yana kara samun goyon baya a tsakanin 'ya'yan jam'iyyar Zanu PF mai mulkin kasar

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Wannan ne karon farko da Mista Mugabe yake fuskantar babban kalubale a tsawon mulkinsa na shekara 37

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Shugaban kungiyar tsofaffin sojojin kasar, Christopher Mutsvangwa ne ya bukaci al'ummar kasar da su fito zanga-zangar adawa da mulkin Mista Mugabe a ranar Asabar

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Wasu masu sa ido sun ce har yanzu Mugabe mai shekara 93, yana son ci gaba da mulkinsa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Sojojin Zimbabwe sun yi wa Shugaba Mugabe daurin talala a babban birnin kasar Harare