Yadda mutane ke mutuwa wajen daukar kansu hoto a India

Vishwas G drowned in a temple pond as his friends took a selfie Hakkin mallakar hoto Bangalore Photo Agency
Image caption Vishwas G ya nutse a cikin ruwa yayin da abokansa ke ta faman daukar Selfie

Hukumomi a jihar Karnataka da ke kudancin Indiya suna aikin wayar da kai don gargadin mutane cewa daukar hoton da suke yi na dauki da kanka da aka fi sani da Selfie, ka iya jawo asarar rayuka.

Wakiliyar BBC a Bangalore Geeta Pandey ta ce, bukatar wayar da kan ta taso ne bayan da wasu dalibai hudu suka mutu a baya-bayan nan sakamakon wasu al'amura da suka faru masu alaka da yin Selfie.

A wata safiyar ranar Lahadi a watan Satumba ne, wasu gomman daliban kwaleji suka ziyarci wani wajen bauta mai nisan kilomita 30 daga birnin Bangalore.

Gargadi: Akwai wani hoto da ka iya daga muku hankali daga kasa

An gina wajen bautar ne a shekarar 1932 a kauyen Ramagondlu, kuma mutane na turuwar zuwa ko yaushe, ciki kuwa har da dalibai daga makarantun da ke kusa da shi.

Matasan, wadanda suna daga cikin masu koyon aikin soji, sun shafe baki dayan safiyar suna tsaftace harabar wajen bautar da kuma yi masa ado.

Can da rana ta take, sai suka yanke shawarar shiga cikin tafkin ruwan da ke harabar wajen bautar don yin iyo.

A lokacin da na ziyarci wajen sai wani mai shago da ke wajen Manjunath, yake ba ni labari cewa: "Dukkansu suna cikin farin ciki da nishadi, suna ta dariya da shewa da daukar hoton Selfie."

Amma wannan rana dai ba ta kare ta dadin rai ba. Daya daga cikin daliban mai suna Vishwas ya nutse a cikin tafkin mai zurfin kamu 15.

A cikin daya daga cikin hotunan selfie da samarin suka dauka dai, ana iya hango kansa yana nutsewa cikin ruwan - amma su ba su lura ba don hanlakinsu na kan kamarar da suke daukar selfie din.

Hakkin mallakar hoto Bangalore Photo Agency

Babu wanda ya lura da shi, kuma sai bayan sa'a daya da faruwar lamarin ne sannan suka farga cewa ba ya tare da su.

Sa'a uku bayan nan ne kuma 'yan sanda tare da taimakon jama'ar yankin suka gano gawarsa.

Makonni kadan bayan haka, wani mummunan al'amarin ya sake faruwa a wani layin dogo da ke da nisan sa'a daya daga wannan wajen bautar, inda jirgin kasa ya bi ta kan wasu samari a yayin da suke daukar hoton selfie a kusa da hanyar jirgin.

Wani dalibi Sharad Gowda, da ke zaune kusa da kauyen ya kai ni wajen da abun ya faru, ya kuma yi min bayanin yadda abun ya kasance.

Ya ce: "Na je zan kai kanina makaranta da misalin karfe 8:15 na safe, a lokacin wajen shiru ba kowa.

"Amma a loakcin da nake dawowa bayan kusan sa'a daya kenan, sai na ga kusan mutum 100 a wajen, don haka sai na tsaya don ganin me yake faruwa.

"Ashe sun fito taya daga daga cikinsu murnar zagayowar ranar haihuwarsa ne."

Wadannan al'amura biyu da suka faru sun matukar girgiza al'ummar Karnataka, kuma gwamnatin jihar ta bukaci matasa da su yi la'akari da abubuwan da ke faruwa su dinga taka tsan-tsan wajen daukar hoton selfie, ganin yadda suke zama sanadin mutane.

Hakan ce ma ta sa a yanzu wasu ke kiran selfie da 'killfies'.

Ministan harkokin yawon bude ido na Karnataka ya shaida wa BB cewa: "Mua aiki don sanya alamun gargadi a wuraren bude ido a gundumomi 11."

"A jikin alamomin za mu rubuta cewa daukar hoton selfie ka iya zama ajali. Za kuma mu fara wani wayar da kai a kafofin sada zumunta nan da mako biyu, a Facebook da Twitter da Instagram da sauran su, don gargadin mutane kan hatsarin da ke tattare da selfie ko killfie."

Hakkin mallakar hoto Asif Saud
Image caption Dalibi Sharad Gowda yana nuna wajen da jirgin kasa ya murtsuke wasu matasa uku a lokacin da suke daukar Selfie

Kusan mutum biliyan 1.1 ne ke amfani da wayoyin sadarwa a Indiya, kuma fiye da mutum 300 ne ke amfani da wayoyin komai da ruwanka.

Kwararru sun ce a yanzu kafofin sadarwa na zamani sun sa matasa suna zurfafawa sosai wajen daukar hotunan selfie, ta yadda suke sayar da ransu wajen yin hakan.

Kuma abun ya fi faruwa a bangaren maza.

Wani bincike da masu bincike na Jami'ar Carnegie Mellon da kuma Cibiyar Sadarwa ta Indraprastha da ke Delhi suka yi, ya gano cewa, Indiya ce kasar da aka fi samun yawan mace-mace sakamakon daukar hoton selfie fiye da ko wacce kasa a shekarun baya-bayan nan.

Sun bayyana cewa za a iya kare irin wannan ibtila'i ta hanyar daina daukar hoton Selfie.

Hakkin mallakar hoto Bangalore Photo Agency
Image caption Jirgin kasa ya bi ta kan Prabhu da Prateek da Rohith a yayin da suke daukar hoton Selfie

Mutane da dama sun mutu sakamakon daukar hoton Selfie, inda jirgin kasa ya bi ta kan wasu ko fadowa daga waje mai tudu, ko nutsewa a ruwa ku ma ruwan ya tafi da su.

A watan Yuni ne 'yan sanda a garin Moradabad da ke arewacin Indiya suka yi barazanar kai mutane da suke da tsananin son daukar hoton selfie gidan yari, in dai har an kama su suna daukar selfie din a kan hanyar jirgin kasa ko gadojin sama ko a lokacin da suke tafiya a cikin mota.

Kuma a shekarar da ta gabata ne 'yan sanda a birnin mUmbai da ke yammacin kasar suka fara sanya wasu alamu a wasu wurare na yawon bude ido da ke nuna cewa an haramta daukar selfie a wajen, bayan da wata budurwa mai shekara 18 ta nutse a kofi yayin da take daukar Selfie.

Amma ministan yawon bude ido na jihar Mr Kharge, ya ce zai yi matukar wahala a sanya alamu a wasu kebantattun wurare, don kuwa masifar na iya faruwa a ko ina.

"Akwai barzanar wannan abu ya faru a ko ma ina ne. Zai iya faruwa a shahararrun wuraren yawon bude ido kamar tsaunin Nandi ko madatsar ruwa, sannan kuma zai iya faruwa a hanyar jirgin kasa ko ma a barandar gidanka.

"Kuskure wa tsallake matakala daya daga benen gidanka ma yayin daukar selfie na iya jawo mutuwa.

"A shirinmu na wayar wa da mutane kai, za mu gaya musu cewa yana da kyau ka mallaki wayar komai da ruwanka, amma fa dole ne ka san yadda za ka yi amfani da ita cikin hankali da nutsuwa."