Wanda zai gaji Mugabe ya dawo daga gudun hijira

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Yadda 'yan Zimbabwe suka yi murnar yin murabus din Mugabe

A ranar Laraba ne tsohon mataimakin shugaban kasar Zimbabwe, wanda korar da Robert Mugabe ya yi masa ta jawo al'amura da yawa a kasar, ciki har da murabus din Mugaben, ya dawo daga gudun hijirar da ke a Afirka Ta Kudu.

Emmerson Mnangagwa, ya gudu Afirka Ta Kudu ne mako biyu da suka gabata, kuma shi ne za a rantsar matsayin sabon shugaban Zimbabwe a ranar Juma'a.

Korar tasa ta jawo jam'iyya mai mulki da kuma manyan sojoji suka shiga cikin batun, wanda ya kawo karshen mulkin Mista Mugabe na tsawon shekara 37.

Labarin murabus din nasa ya jawo muran da farin ciki a kasar a ranar Talata da daddare.

Sanarwar yin murabus din nasa ta zo ne a yayin da aka karanta wasikar a zauren majalisar dokokin kasar.

Wasikar da Mista Mugabe ya aika ta ce ya dauki matakin ne a kashin kansa domin bayar da dama a samu sauyin gwamnati cikin ruwan sanyi.

Wani mai magana da yawun jam'iyyar Zanu-PF ya ce Mista Mnangagwa mai shekara 71, zai karasa wa'adin mulkin Mista Mugabe har sai lokacin zaben da za a yi a watan Satumbar 2018.

Gidan talbijin na kasar ya ce za a rantsar da shi a ranar Juma'a.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A baya kadan Emmerson Mnangagwa ya kasance babban na hannun damar Robert Mugabe

Mista Mnangagwa wanda ake kira da 'Kada' saboda iya dabarar siyasa, ya fitar da wata sanarwa a lokacin da yake gudun hijira, inda yake kira ga al'ummar Zimbabwe da su hada kansu don sake gina kasar.

Mr Mnangagwa ya shaida wa wata kafar yada labaran Zimbabwe a ranar Talata cewa: "Idan muka hada kai za mu tabbatar da mika mulki cikin ruwan sanyi don karfafa dimokradiyyarmu, mu kuma bude sabon babi ga 'yan Zimbabwe a samu hadin kai da zaman lafiya."

Ya sadu da shugaban kasar Afirka Ta kudu kafin ya bar Zimbabwe.

Labarai masu alaka

Karin bayani