Kalli bidiyon otel din da Saudiyya ta mayar gidan yari
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

BBC ta ziyarci Ritz Calton otel wanda Saudiyya ta mayar gidan yari

A farkon watan nan ne hukumomin Saudiyya suka tsare wadansu 'yan gidan sarautar kasar ciki har da ministoci hudu a birnin Riyadh.

Ritz Calton otel ne da shugabannin kasashe da firaministoci ke sauka, domin masauki ne na hamshakan attajirai, sai dai yanzu ya koma wani gidan yarin kasaita ga yarimomin gidan sarautar.

A wannan otel din ne Shugaban Amurka Donald Trump ya sauka lokacin da ya kai ziyararsa ta farko kasar a watan Mayun da ya gabata.

Labarai masu alaka