Ayatollah Khamenei na Iran 'Hitler' ne – Yariman Saudiyya

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Ko Saudiyya za ta yi yaki da Iran?

Yarima mai jiran gadon masarautar Saudiyya, Muhammad bin Salman, ya bayyana jagoran addinin Iran a matsayin sabon Hitler na Gabas ta Tsakiya.

Yariman ya yi wadannan kalamai ne a yayin da dangantaka ke kara tsami tsakanin kasashen biyu.

Da yake gugar zana, Muhammad bin Salman ya ce yana da matukar muhimmanci a guji maimaita irin abun da ya faru a nahiyar Turai, a Gabas Ta Tsakiya.

Saudiyya da Iran dai manyan abokan fada ne, kuma a baya-bayan nan ana samun ci gaba da nuna yatsa tsakaninsu.

Zuwa yanzu dai Iran ba ta ce komai ba dangane da kalaman yariman Saudiyyar.

Yarima mai jiran gadon ya shaidawa jaridar New York Times cewa, "Ba ma son a sake samun sabon Hitler a Iran kamar yadda ya taba faruwa a Turai," ya fada yana mai alakanta hakan da Ayatollah Ali Khamenei.

Yarima Muhammad ya kuma yi tsokaci kan yaki da cin hanci da yake a kasarsa, inda ya ce yakin da yake yi da cin hanci ba wai yanayi ba ne don neman mukami, tun da yawancin wadanda ake zargi da aka kama sun masa mubaya'a.

Yariman ya ce kiyasin kadarorin da aka bankado zai kai kusan dala biliyan 100.

Yarima mai jiran gadon ya kuma yi bayani a kan irin manufofinsa na sassauta dokokin addinin musulunci wanda ya ce Manzon Allah SAW ma yafi son haka.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Abubuwa biyar kan Yarima mai jiran gadon Saudiyya

Tun shekara biyu da suka gabata dai, Mohammed bin Salman, mai jiran gado, ya sake jan layi tsakanin mu'amalar kasarsa da Iran.

A farkon watan nan ne, ya zargi Iran da son jawo yaki a kasarsa, inda ya ce ita ce ta sa 'yan tawayen Yemen suka kai harin makami mai linzami babban birnin kasar, Riyadh.

Amma Iran ta yi watsi da zargin.

Saudiyya dai kasa ce da mafi yawan mabiyanta Musulmai ne 'yan Sunni, yayin da mafi yawan 'yan Iran 'yan Shi'a ne.

Saudiyya na zargin Iran da taimakawa mayakan sa kai na Houthi masu bin tafarkin Shi'a a Yemen, inda Saudiyyar ke jagorantar wata gamayyar kawance, da ke ta tafka yaki tun shekarar 2015.

Iran dai da mayakan Houthi sun yi watsi da wannan tuhuma.

An yi ta zargin Saudiyya da damalmala rikicin da ke faruwa a Yemen, inda mutane ke cikin halin ha'ula'i, da Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana da mafi muni da aka taba samu a duniya.

Saudiyya ta kuma yi gargadi kan yadda Iran ke shiga cikin al'amuran Iraki, inda mayakan sa kai ke fafatawa da mayakan IS, da kuma Syria, inda sojojin Iran din ke taimakon Shugaba Bashar al-Assad don ya samu nasara a yakin basasar kasar.

Dukkan kasashen biyu suna zargin juna da son kawo rashin zaman lafiya a Lebanon, inda Firai ministan da Saudiyya ke goyon baya ya jagoranci wata gamayyar kawance da ta hada da kungiyar Hezbolla da Iran ke goyon baya.

A baya-bayan nan ne Firai minista, Saad Hariri ya sanar da cewa ya dakatar da janyewarsa, inda yake zargin Iran da Hezbollah jawo sabani, yayin da Iran kuma ke zargin Saudiyya da rura wutar rikicin.

Labarai masu alaka