Kalli hotunan bikin Gasar Hikayata ta BBC ta bana

Gidan yada labarai na BBC Hausa ya karrama matan da suka lashe Gasar Hikayata da aka gudanar kan kagaggun labarai a bana.

Zauren bikin Hikayata ta bana
Bayanan hoto,

Maimuna da Balkisu da Habiba da kuma Hindatu wadanda suka lashe Gasar Hikayata ta shekarar 2017

Bayanan hoto,

An gudanar da bikin karrawar ne a otel din Sheraton da ke Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya ranar Juma'a

Bayanan hoto,

Wannan ne karo na biyu da BBC ta sanya gasar kagaggaun labarai ta mata zalla

Bayanan hoto,

Bikin ya samu halartar manyan baki daga ciki da wajen Najeriya

Bayanan hoto,

Shugaban Sashen Hausa na BBC Jimeh Saleh yayin da yake gabatar da jawabi a zauren taron

Bayanan hoto,

Shugaban ya ce ana aikin yin wani kundi wanda za a wallafa kuma zai kunshi labarai da suka yi zarra a bara da kuma bana

Bayanan hoto,

Bikin ya samu halartar tsohon Shugaban Sashen Hausa na BBC Mansur Liman

Bayanan hoto,

A bara ne aka fara kirkiro Gasar Hikayata ta mata zalla

Bayanan hoto,

Maimuna Idris Sani Beli, wadda ta zama gwarzuwar gasar a bana, ta samu lambar yabo da kuma $2,000

Bayanan hoto,

Balkisu Sani Makaranta ce ta zo ta biyu, kuma ta samu lambar yabo da dala $1,000

Bayanan hoto,

Habiba Abubakar da kuma Hindatu Sama'ila Nabame Argungu (daga dama), wadanda suka yi na uku, sun samu lambar yabo da $500