Na fada wa Buhari halin da talakawa suke ciki – Sheikh Bala Lau

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Har ayoyin Al-Kur'ani sai da na jawo wa Buhari – Bala Lau
  • Latsa alamar da ke sama don kallon bidiyon hirar

Shugaban Kungiyar Jama'atu Izalatul Bid'ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS), Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya shaida wa BBC dalilin da ya kai su fadar shugaban Najeriya.

A farkon watan nan ne wadansu malaman addinin Musulunci a kasar suka kai wa Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ziyara a fadarsa da ke Abuja.

Sheikh Bala Lau ya ce dalilin zuwansu fadar bai wuce batun cewa shugaban ya kwashe lokaci mai tsawo bai sadu da malaman addinin ba, tun gabanin ya fara jinya a farkon shekarar nan.

Malamin ya bayyana hakan ne lokacin da ya kawo mana ziyara a ofishinmu na Landan ranar Alhamis tare da rakiyar Sheikh Kabiru Gombe.

Hakkin mallakar hoto Nigeria Presidency
Image caption A farkon watan ne wane wadansu malaman addinin Musulunci suka kai wa Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ziyara a fadarsa da ke Abuja

"Ba kawai malunma na addinin Musulunci shugaban ya gani ba. A'a har da ma malaman addinin Kirista ya gana da su a lokacin," in ji shi.

Ya ci gaba da cewa: "Babu shakka mun shaida masa halin da talakawa suke ciki har ayoyin Al'kur'ani sai da na karanta masa."

Har ila yau malamin ya ce sun bukaci shugaban da ya rika kawo sauki a cikin shugabancinsa.

Kuma ya ce shugaban ya ba su tabbacin aiki da shawarwarin da suka ba shi.

Za ku iya kallon cikakkiyar hirar da BBC ta yi da Sheikh Bala Lau da kuma Kabir Gombe idan kuka latsa nan.

Labarai masu alaka